Mahaifiyar Jarumi Haruna Talle Mai Fata Ta Rasu

Haruna Talle Mai Fata (Instagram/Haruna Talle Mai Fata)

Tuni dai abokansa a masana’antar ta Kannywood suka yi ta taya jarumin alhinin wannan rashi ta hanyar mika sakonnin ta’aziyyarsu.

Mahaifiyar jarumin Kannyood, Haruna Talle Mai Fata ta rasu kamar yadda tauraron ya wallafa sakon a shafinsa na Instagram a ranar Laraba.

“Innalillahi wa Inna’ilaihirraji'un, Allah ya yi wa mahaifiyata rasuwa yau, za’ a yi jana'izarta a kofar gidanta da ke Kano Mill Tara." In ji Haruna

Tuni dai an riga an yi jana’izar marigayiyar a birnin Kanon Najeriya.

Tuni kuma abokansa a masana’antar ta Kannywood suka yi ta taya jarumin alhinin wannan rashi ta hanyar mika ta’aziyyarsu.

“Muna addu’ar Alla ya jikanta ya gafarta mata kurakuranta, ya sa Aljanna ce makomarta. Idan kuma ta mu ta zo, Allah ya sa mu cika da kyau da imani.” In ji Ali Nuhu.

“Allah Ubangiji ya gafarta mata, ya sa mutuwa hutu ce a gare ta
Allah ya kyautata Kkrshenmu.” In ji jaruma Aisha Humaira.

“Allah ya gafarta mata, ya sa ta huta Albarkacin Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi wasallam da Alkur’ani Mai Girma.” In ji jarumi Sadiq Ahmad.

Ita kuwa Madam Korede cewa ta yi "Innalillahi, Allah ya gafarta mata sorry Haruna."