Solskjaer Ya Dauki Dauki Alhakin Shan Kashi

  • Murtala Sanyinna

Kocin Manchester United Ole Gunner Silskjaer.

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar Manchester United ta Ingila Ole Gunnar Solskjaer, ya ce an sami kura-kurai da dama a bangaren 'yan wasansa, a wasan su na gasar Premier a jiya Lahadi.

Solskjaer ya dauki alhakin mummunan kashin da kungiyar ta sha a hannun Tottenham din da zunzurutun ci 6-1.

United wadda ke karbar bakuncin gasar a filin ta na Old Trafford, ita ce ta soma zura kwallon, to amma kuma Tottenham ta farke cin, ta kuma zura kwallon ta biyu, kafin alkalin wasan ya ba da jan katin kora ga dan wasan United din Anthony Martial, tun a minti na 28 a cikin rabin lokacin wasan na farko.

'Yan wasan Tottenham na murnar zura kwallo

Duk da yake kocin kungiyar ya ce shi ke da alhakin kashin da suka sha sakamakon wasu kura-kurai daga bangaren ‘yan wasa, to amma kuma ya ce korar dan wasan na su daga wasan ne ya karya musu lago a wasan.

Wannan ne kashi mafi muni da kungiyar ta sha a kakanni wasanni na baya-bayan nan, a daidai lokacin da take kokarin murmurewa, bayan soma sabuwar kakar wasanni ta bana a cikin kalu-bale.