Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea Ta Lallasa Crystal Palace


Chelsea

Kungiyar kwallon kafar Chelsea ta Ingila ta lallasa Crystal Palace da ci 4-0 a wasan su na gasar Premier a yau Assabar

Chelsea din ta zuba kusan dukkan sababbin sayen ‘yan wasan ta a wasan na yau, ciki har da na baya-bayan nan, wato mai tsaron gida Edward Mendy.

Kungiyar ta sha kashi a wasannin ta 2 na baya-bayan nan, inda Tottenham ta doke ta ta hanyar bugun penarity a gasar Carabao, bayan da ta ta yi waiwayen baya ta yi kunnen doki da kungiyar West Brom da ci 3-3.

Mai horar da 'yan wasan Chelsea Frank Lampard
Mai horar da 'yan wasan Chelsea Frank Lampard

A daya wasan ta Premier ta yau kuma, Everton ta doke Brighton da ci 4-2, yayin da Leeds United da Manchester City suka yi kunnen doki da ci 1-1.

Facebook Forum

Diego Maradona 1960-2020
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:07 0:00
Karin bayani akan Diego Maradona
XS
SM
MD
LG