Tashin Bom a Jos Nigeria ya Kashe Mutane Biyu

In this image taken from TV showing the bodies of victims of inter-faith violence as a crowd gathers around, in the town of Dogo Nahawa, Nigeria, south of the city of Jos (File Photo)

‘Yan sanda a birnin Jos, jihar Plateau Nigeria, sun bada rahoton kara samun fashewar bom a Jos jihar Plateau lokacin da wasu matasa dauke da bom din a kan babur yayi bindiga.

‘Yan sanda a birnin Jos, jihar Plateau Nigeria, sun bada rahoton kara samun fashewar bom a Jos jihar Plateau lokacin da wasu matasa dauke da bom din a kan babur yayi bindiga, anji kwamishinan ‘yan sandan jihar Plateau Abdulrahman Akano yana bayyanawa manema labarai cewa bom din ya tashi ne a dai dai lokacin da matasan ke dauke dashi suna sintiri a kan babur a unguwannin birnin Jos inda Musulmi da Kirista ke yawaita baiwa hamata iska.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa yau lahadi da safe ne fashewar ta afku a kusa da wata mujami’ar birnin Jos. Jami’an tsaron Nigeria sun kakkafa shingaye domin hana mutane kaiwa da komawa a yankin, amma hayaki ya turnuke sararin samaniyar yankin. Ba’a sami rahoton wata jikkata ba. Birnin Jos ya jima yana fama da tashe-tashen hankula, kama dai bisa dalilai na rabon fili, ko ayyukan yi da kuma harkokin siyasa. Mutane da dama suna rasa rayukansu.