'Yan sanda Sun Ceto Biyu Daga Cikin Daliban Makarantar Bethel

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai.

A ranar 8 ga watan Yuli, ‘yan bindiga suka far wa makarantar wacce ke karamar hukumar Chikun, suka yi awon gaba da dalibai sama da 100.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, jami’an ‘yan sanda sun kubutar da biyu daga cikin daliban makarantar sakandaren Bethel Baptist da aka sace a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar.

A ranar 8 ga watan Yuli, ‘yan bindiga suka far wa makarantar wacce ke karamar hukumar Chikun, suka yi awon gaba da dalibai sama da 100.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa, a daren Laraba ‘yan sanda suka ceto biyu daga cikin su a yankin Rijanna da ke kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hukumomin tsaro a jihar sun ce an kai daliban wani asibitin ‘yan sanda don a duba lafiyarsu.

Karin bayani akan: Nuhu Bamalli, Nasir El-Rufai, Kaduna, dalibai, ‘yan bindiga, Nigeria, da Najeriya.

Kubutar da karin dalibai biyun, na nufin an yi nasarar ceto uku kenan.

A makon da ya gabata, ‘yan sanda sun kubutar da daya daga cikin daliban a wani daji kamar yadda Channels ya bayyana.

Tun gabanin hakan, ‘yan bindigar da suka sace daliban, na neman a biya kudin fansa naira miliyan 60.

Karin bayani akan: Bethel Baptist, dalibai, jihar Neja, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Kaduna ta kasance daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga da ke garkuwa da dalibai da sauran jama'a.

A ‘yan watanni baya-bayan nan an sace dalibai a makarantar koyar da ilimin kula da gandun daji, da jami’ar Greenfield da kuma kwalejin kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli duk a jihar ta Kaduna.

A makwanbciyarta jihar Neja, ‘yan fashin dajin na rike da daliban Islamiyya sama da 100 da suka sace a garin Tegina tun a karshen watan Mayu.

Iyayen Daliban Da Aka Sace A Najeriya, Aun Gudanar Da Addu’o’i

Your browser doesn’t support HTML5

Iyayen Daliban Da Aka Sace A Najeriya, Aun Gudanar Da Addu’o’i

Iyayen daliban Bethel da aka sace a Najeriya sun taru a makarantar

Your browser doesn’t support HTML5

VOA60 AFIRKA: Iyayen daliban Bethel da aka sace a Najeriya sun taru a makarantar