Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Daliban Kwalejin Nuhu Bamalli, An Sace Mutum 9 A Kaduna


Dalibai da malaman kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da 'yan bindiga suka sako

Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa an sako dalibai 6 da malamai 2 da ‘yan bindiga suka sace a kwalejin fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a jihar ta Kaduna.

‘Yan bindigar sun sako mutanen ne a cikin daren jiya Alhamis a wani wuri da ba’a bayyana ba a Kaduna, bayan sun kwashe kusan wata daya a hannunsu.

Tashar talabijin ta CHANNELS ta ruwaito jami’in hulda da jama’a na makarantar fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli, Abdullahi Shehu, yana cewa an sako mutanen ne bayan da iyayensu suka daidaita da ‘yan bindigar.

Dalibai da malaman kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da 'yan bindiga suka sako
Dalibai da malaman kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da 'yan bindiga suka sako

To sai dai bai yi cikakken bayani akan daidaitawar ba, da kuma ko an biya kudin fansa ba.

Idan za’a iya tunawa dai ‘yan bindigar sun kai hari a kwalejin fasaha da kere-kere ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a ranar 11 ga watan Yuni, inda suka kashe dalibi daya, suka kuma yi awon gaba da daliban da malamansu.

Karin bayani akan: Nuhu Bamalli, Nasir El-Rufai, Kaduna, dalibai, ‘yan bindiga, Nigeria, da Najeriya.

A wani labarin mai kama da wannan kuma wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Warkan da ke yankin karamar hukumar mulkin Zangon Kataf a jihar ta Kaduna da sanyin safiyar yau Juma’a, inda suka yi awon gaba da mutane 9, bayan sun jikkata wasu da dama.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa maharan da ke da yawan gaske, sun kai farmakin ne da misalign karfe 2 na safe, inda kuma suka cinnawa gidaje da dama wuta, a yayin da jama’a suke bacci.

Kofar Kwalejin Kimiyya ta Nuhu Bamalli a Kaduna (Hoto: Facebook/ Channels TV)
Kofar Kwalejin Kimiyya ta Nuhu Bamalli a Kaduna (Hoto: Facebook/ Channels TV)

Majiyoyin sun ce jama’ar garin sun shiga rudani sosai, a yayin da kuma mutanen da aka raunata suke karbar kulawar likitoci a wani asibiti da ba’a bayyana ba.

Ya zuwa yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna bata ce komai akan harin ba tukunna.

Jihar ta Kaduna na fuskantar hare-hare a ‘yan kwanan nan, inda ake kashe mutane da kuma sace wasu musamman dalibai a makarantu.

Masu fashin baki na ta’allaka lamarin da takaddamar da ake hasashen ta taso tsakanin gwamnatin jihar da ‘yan bindiga tun sa’adda gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya ce ba zai sulhunta da ‘yan bindiga ba, duk da yake dai wasu rahotannin da ba’a tabbatar ba na cewa gwamnan na duba yiwuwar sauya shawara akan matsayar ta shi a halin yanzu.

Hukumomin Nijar Sun Fara Kwashe ‘Yan Kasar Masu Bara A Titunan Wasu Kasashe

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG