A Kasar Nijar mayakan Boko Haram fiye da 100 ne suka kammala wani shirin fitar da su daga cikin wannan haramtacciyar akida, bayan kamala wani horo a kudu maso gabashin kasar, domin fadakar da su.
A kasar Finland, jam'iyyar SDP ta zabi Sanna Marin mai shekaru 34 da haihuwa wadda Ministar zirgazirga ce, a matsayin Firamistar kasar a jiya Lahadi.
Ma’aikatar kula da harkokin mata, ta kaddamar da wata rajista da za ta kunshi sunayen mutanen da kotu ta same su da laifin aikata fyade. Dabarar yin hakan ita ce, don a fargar da jama’a su san yadda za su yi mu’amulla da masu wannan mummunar dabi’a.
A kasar Mali kuma an yi jinjina ta musamman a matakin kasa ga gawarwakin sojojin Faransa 13 da aka kashe a kasar, bayan faduwar jirgin sama kafin aika su zuwa Faransa a ziya litinin.
A kasar Iraki, mata da dalibai sun yi zanga zanga a birnin Basra mai arzikin man fetur, inda su ka lashi takobin cigaba da yin zanga zanga, yayin da kungiyar zanga-zangar, wadda ta kai watanni biyu da kahuwa.
Matakin rufe iyakokin Najeriya da kasashen da ke makwabtaka da ita, ya jefe wadannan kasashe cikin mawuyacin hali, yayin da rahotanni ke nuna cewa, a cikin gida ma ba a tsira ba, kamar yadda wani dan kasuwa Emeka Uguoke ya ce, hakan, ya sa farashin shinkafa ya yi tashin goron zabi.
A kasar Senegal ana shirin kaddamar da karo na farko na Babban Bukin Dakar a dandalin Place de la Nation da ke birnin Dakar, inda ake fatan baje koli tare kuma da tallata al'adar Senegal.
A kasar Kenya, jami'ai a kasar na cewa yawancin wadanda suka mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a yammacin kasar ya kai 65, yayın da gwaman jihar Pokot wadda ta fi kowane yanki lalacewa ke cewa mutane fiya da dubu 80 ne lamarin ya shafa.
A kwanan nan Muryar Amurka ta sami bakuncin wani shahararren mawaki dan kasar Mali mai suna Salif Keita. Duk da cewa Keita zabiya ne babu abinda ya hana shi cimma burinsa a rayuwa. Ga fassarar hirar da Abdul’aziz Adili Toro ya yi da shi
dan tsohon shugaban kasar Jamus Jamus Von Weizsaecker ya mutu bayan da aka daba mai wuka, a yayin da yake gabatar da mukala a asibitin Schosspark-Klinik da ke Berlin babban birnin kasar inda yake aikin likita. Yanzu haka hukumomi sun tsare wani bajamushe mai shekaru 57.
A Ethiopia, an fara zaben raba gardama a yankin kudancin kasar a jiya Laraba, kan ko ‘yan kabilar Sidama su kafa gwamatinsu ko akasin hakan, zaben da ka iya zaburar da wasu kabilu su bi sahu.
A kasar Senegal an bude taro na musamman karo na shida akan tsaro da kuma zaman lafiya a Dakar baban birnin kasar. Ana kyautata zaton mutane da dama za su hallara, ciki har da sojoji a tawagogin diflomasiyya.
Najeriya inda Gracious David West, wanda aka zarga da kisan mata goma, ya gurfana a kotu a birnin Fatakwal. An dai dage ranar shari'ar zuwa Alhamis 'yan mintoci kawai da isowarsu kotun. Tuni dai ya amsa cewa ya aikata tara daga cikin zarge-zarge goma kisan kan.
Shugaban jam'iyyar Lumana kuma madugun 'yan adawa a Nijar Hama Amadou ya samu dawowa gida bayan shekaru biyar yana gudun hijira a kasashen waje. Ana iya cewa, dawowar ta shi nasaba da rasuwar mahaifiyarsa a cikin wata Oktaba da ya gabata. Issoufou Issaka yayi karin bayani.
Domin Kari