Lamarin ya auku ne bayan wani hastari da motar hukumar, a lokacin da jami'anta suke bin wani da suke zargi da daukar shinkafa daga kasar Kamaru zuwa Najeriya ba tare da izini ba, a yankin Hayingada da ke karamar hukamar Girei inda mutum hudu suka mutu bakwai kuma suka jikkata.
An sake arangama tsakanin 'ya'yan kungiyar Ansaru da kuma 'yan-bindiga a yankin Damarin karamar hukumar Birnin Gwari sakamakon da aka kashe 'yan bindiga biyar.
Anyi zaman sulhu stakanin kanfanin suga na Dangote dake garin Numan a Jihar Adamawa inda zaman ya samu halartan sarakunan gargajiya na yankin gaba daya da kuma shugaban kamfanin Dangoten Alhaji Aliki Dangote.
Sashen tattalin arziki da zamantakewa na Majalisar Dinkin duniya ya fitar da wani rahoto dake nuna cewa yawan mutane a Najeriya ya kai miliyan 216 a shekarar 2022, da hakan ya kai kashi 2.7 na al’ummar duniya.
Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta bayyana cewa za ta fara tattaunawa da hukumar aikin hajji da umrah ta Saudiyya don fara yarjejeniyar aikin hajjin badi.
A wata sanarwar da gwamnatin Chadi ta fitar ta ce mayakan Boko Haram sun kashe sojojin Chadi akalla 10 a wani hari da suka kaiwa wata rundunar soji a yankin tafkin na Chadi da ke kusa da iyakar Najeriya ranar Talata.
An raba kasashen da za su fafata din ne zuwa rukunoni 4, inda Senegal ta ke cikin rukunin A, Tunisia a rukunin D. Morocco na rukunin F, Kamaru a rukunin G, sai Ghana take rukunin H. Qatar mai masaukin baki ce za ta buga wasan farko da Ecuador a filin wasa na Al Bayt
Biyo Bayan Korafe Korafe, Majalisar Dattawan Najeriya ta kafa wani Kwamitin wucin gadi mai dauke da mutum 7 da zai gudanar da bincike akan yadda aka kasafta Naira biliyan 500 ga shiyoyi shida na kasar daga bankin raya kasa na Najeriya.
A wata hira da shugaban kungiyar makafi ya kwatanta girman wannan matsala da kuma hanyoyin da yake ganin idan aka bi su za a warware wannan kulli.
Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya umarci jami’an tsaro da su kamo ‘yan bindigan da suka hallaka mutum 11 a kauyen Maikatako da ke karamar hukumar Bokkos.
‘Yan bindiga sun kashe mutum 11 sun kuma yi awon gaba da shanu sama da dubu daya a yankin Gombe Dela da ke karamar hukamar Karim Lamido a Jihar Taraba.
Wata kotu a Najeriya ta tuhumi wasu mutane 26 da laifin hada baki wajen aikata laifin kanruwa da kuma yunkurin yin cinikin danyen mai ba bisa ka'ida ba, bayan da hukumomi suka zargi jirginsu da shiga sararin ruwan Najeriya ba tare da izini ba.
Gwamnatin jihar Borno ta kai dauki ga iyalan mayakan CJTF da aka kashe a yakin da suke yi da ‘yan ta’addan Boko Haram, da wasu rahotanni
Tunda farko dai babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta yi zargin cewa gungun ‘yan bangar siyasa sun kai wa tawagar dan takararta hari a birnin Maiduguri jim kadan bayan wani gangamin kamfe inda aka jikkata magoya baya har arba'in da bakwai tare da lalata motocin da ke cikin tawagar.
Sakacin gwamnati da al'ummar Najeriya na daga cikin abubuwan da suka kawo bazuwar matsalolin rashin tsaro a Arewa maso Gabas da sauran wurare daban daban.
Domin Kari