A yayin ziyarar shugaba Bola Tinubu zuwa jihar Borno, ya kaddamar da wasu motocin sufuri da gwamnatin Farfesa Baba Gana Umara Zulum ta sayo a kwanan nan domin sauwaka wa al’ummar jihar zirga-zirga.
Dakarun rundunar Operation Hadin Kai ta sojojin Najeriya sun ceto wasu 'yan mata biyu da aka sace daga karamar hukumar Chibok ta jihar Borno a watan Afrilun 2014.
Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Jaji Olola Abdulganiyu, ya kai ziyarar gane wa ido da jajantawa kan gobarar da ta cinye manyan kasuwanni biyu a Maiduguri, inda ya shawarci ‘yan kasuwan da su kafa kungiyar ‘yan kwana-kwana ta sa kai don dakile matsalar.
‘Yan Najeriya da dama sun yi tsammanin samun maslaha kan matsalar karancin takardun kudade bayan kotun koli ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da N200, N500 da N1000 da babban bankin CBN ya sauya fasalinsu, tare da shata wa’adin 10 ga Fabrairu, to amma wasu ‘yan kasar na cewa tana kasa tana dabo
‘Yan ta’addan Boko Haram sun kashe mutane 26 da suka hada da dan sanda daya da masunta a wasu hare-haren ba zato ba tsammani a garuruwan jihar Borno.
Bayanai sun yi nuni da cewa giwayen sukan far gonakin mazauna yankin ne da tsakar dare su cinye musu amfanin gonakinsu.
Wannan yajin aiki ka iya haifar da matsalar karancin man a yankin arewacin kasar ciki har da Abuja, babban birnin Najeriya kamar yadda masu lura da al'amura suka bayyana.
Kaddamar da ofishin jami'yyar na zuwa ne, kwanaki uku bayan da rahotanni suka nuna cewa ‘yan sanda a jihar sun rufe ofishin na NNPP da ke garin Maiduguri.
Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ya ba da umurnin samar da aiki ga 'ya'yan malamin nan da aka kashe Alhaji Goni Aisami a karkashin gwamnatin Jihar.
Bayan kamala zaben fidda gwani a tarayyar Nageriya kama dana 'yan majalisa dokoki har da na shugaban kasa, yanzu ana iya cewa kallo ya koma kan neman 'yan takarar maitamakin shugaban kasa da ke iya zamowa baban kallobale a Najeriya.
Burodi na daya daga cikin nau’ukan abinci da ake yawan amfani da shi a sassan duniya.
Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana goyon bayan matakan da gwamnatin jihar Borno ta dauka na karbar mayakan kungiyar Boko Haram da su ka ajiye makamai su ka rungumi zaman lafiya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bayar da iyakacin kokarinta na ci gaban kasar har zuwa watan Mayu, 2023, yana mai jaddada cewa zai mika mulki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Da alamar bakon da aka raka shi na neman ya dawo, saboda wasu da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun cillo abubuwa masu tarwatsewa, ciki har da masu kama da rokoki, kan birnin Maiduguri, inda aka ga barna sosai. Babu rasa rai amma.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware 5 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za a duba halin da malamai suke ciki a sassan duniya.
Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta kame wasu mutane goma da ake zargin aikata laifuka daban-daban da ya kama da na fashi, da zamba cikin aminci da kuma wasu da aka kama da tabar wiwi mai yawan gaske.
A cikin makonnan ne Gwamnatin Jihar Borno ta rufe wasu sansanonin 'yan gudun hijira biyu dake cikin garin Maiduguri cikin 27 da ake da su, inda tayi jigilar 'yan gudun hijiran zuwa wani kauye da ake kira Auno dan tsugunanar da su a wasu rukunin gidaji da ta gina guda 580.
A yau a ke sa ran tattara ra'ayoyin 'yan Najeriya game da gyaran fuska cikin dokokin tsarin mulkin kasar da a ke ganin akwai bukatar sake duba wadannan dokokin.
A yammacin ranar Talata, wasu da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kai hari kan unguwar Jiddari Polo dake garin Maiduguri inda suka dinga harba manya-mayan bindigogi da kuma wasu ababe masu fashewa.
Kimanin mutum 37 ake fargabar sun rasa rayukansu sakamakon wasu hare-hare da wasu mayakan Boko Haram suka kai kauyen Ajari da ke karamar hukumar Mafa a jihar Borno.
Domin Kari