Gobara ta sake afkawa sansanin ‘yan gudun hijira tare da lakume gidaje 83 a garin Maiduguri na jihar Borno. Lamarin da ya jefa ‘yan gudun hijirar cikin mawuyacin hali.
Babban Hafsan sojan kasa na Najeriya Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya ce za su yi su ga cewa sun gama da mayakan Boko Haram da ke arewa maso gabashin Najeriya da ma sassan kasar baki daya.
Wata gidauniya da ke rajin kare hakkin mata da kananan yara da ake kira Al'amin Foundation da ke cikin garin Maiduguri ta yi kira ga sababbin manyan hafsoshin sojin kasar da su yi wa Allah su binciki batun wasu mutane su 9600 da aka ce suna tsare a hannun jami'an sojan Nijeriya.
Matan da ke zaune a sansanan 'yan gudun hijira na cikin gida a jihar Borno sun bayyana takaicin ganin yadda su ke ci gaba da zama a takure shekaru bayan barin muhallansu sakamakon hare-haren Boko Haram.
Jihar Yobe ta shiga sahun wasu jihohin arewacin Najeriya wajan rufe dukkannin makarantun kwana da ke fadin jihar don gudun afkawa makarantu da wasu 'yan bindiga ke yi.
An yi jana'izar wasu mutane da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka yi musu yankar rago a Maiduguri.
Da yammacin jiya da misalin karfe shida na maraice ne mazauna birnin Maiduguri suka fara jin karar wasu ababe masu fashewa kamar bam.
Rahotanni daga jihar Borno na nuna cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun sake kwace garin Marte dake arewacin Borno, tare kwashe makaman jami’an tsaro da kafa tutocinsu.
Ajiya da marace ne wasu da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kai hari garin Gaidam dake jihar Yobe shiyar arewa maso gabashin Nageriya, sai dai al'umman garin Gaidam suka ce maharan basu sha da dadi ba a wajan jami'an tsaro ganin yadda aka fattatake su, wasu maharan sun arce da arsahin bundiga.
Sojojin Najeriya za su yi hadin gwiwa da sojojin kasar Chadi, don yakar ta'addanci a yankin Arewa maso gabas.
Gwamnan jihar Borno Furfesa Babagana Umara Zulum ya ziyarci mahaifarsa da ke Karamar Hukumar Mafa a jihar Borno don ya sabunta rajistarsa ta APC. Bayan nan ne tawagar Mai Kanuribe ta yi hatsarin mota ya rasu.
Tawagar gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ta yi mummunar hatsarin mota yayin da suke komowa Maiduguri inda mutane 3 suka rasa rayukansu.
A kokarin magance matsalar tsaro da garkuwa da mutane don kudin fansa akan tituna, gwamnatin jihar Borno ta dauki nauyin shimfida hanyar Maiduguri zuwa Bama, wadda za ta kai har zuwa wasu kasashen Afirka.
Babban hafsan hafsoshin sojojin Najeriya Manjo Janar Lucky Irabor da sauran manayan hafsoshin kasar sun ziyarci garin Maiduguri a karo na farko kwanaki bayan nada su a mukamansu.
Bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya biya bukatar 'yan Najeriya na ya sauke manyan hafsoshin sojin kasar, ganin sun kasa kawo karshen Boko Haram da sauran miyagu a fadin kasar.
Kungiyar taraiyar yamnacen Afrika da akekira ECOWAS a takaice ta mika wani tallafin abince ga wasu jihohin Arewacen Nigeriya gada takwas ceki har da jihar Borno da yanzu hakkan ke fama da 'yan gudun hijira fiye da miliyan guda.
An yi zana'iyar wasu maharba bakwai da suka gamu da ajalinsu yayin da su ka bi ta kan wani bomb da aka dana a kan hanya
Bayan da jama'ar jahar Borno su ka dandana wahalar katse masu wasu muhimman hanyoyi saboda kokarin tabbatar da tsaro, wanda shi ma bai samu ba, gwamnatin jahar ta ce ba zai yiwu a ce babu riba kuma babu uwar kudi ba.
Shugaba Muhammadu Buhari ya tura wata tawaga karkashin jagorancin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahamed Lawan, don jajanta wa al'ummar jihar Borno kan kisan gillar da aka yi wa manoman shinkafa 43 a kauyen Zabarmari.
Zargin da wani dan Majalisar Dokokin Burtaniya ya yi cewa tsohon Shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon ya arce Ingila da dinbin kudin Najeriya ta na neman zama wata babbar magana,
Domin Kari