Ranar Laraba kungiyar ISIS ta bayyana Abu Musab al-Barnawi a matsayin sabon shugaban kungiyar Boko Haram, amma jim kadan bayan hakan Abubakar Shekau ya kushewa nadin tare da cewa yana nan akan shugabancin kungiyar
Duniya na dada sa ido kan gwaje-gwajen makamai da Koriya Ta Arewa ke yi. An kuma bayyana yankin Pacific da cewa shi ya fi fuskanar barazana.
A cigaba da karfafa gwiwa ga Amurkawa da Shugaba Barack Obama ke yi tun daga kasar Poland bayan kashe-kashen da aka yi a Amurka, ya sake jaddada cewa Amurka ba ta rarrabu ba.
Yayin da bangarori biyu da ke jayayya da juna a Sudan Ta Kudu ke cigaba da fafatawa, duk kuwa da jituwar aka cimma kwanan nan, Amurka ta yi kira ga bangarorin da su kai zuciya nesa.
Yayin da ake cigaba da rufe tafsiran azumin watan Ramadan na bana, Malamai na cigaba da jawabai da zummar ganin darrusan Ramadan sun cigaba da yin tasiri a rayuwar jama'a
A wani al'amari mai nuna alamar an shiga wani babi mai sarkakkiya a yakin da ake yi da Boko Haram, sojojin Najeriya sun kaddamar da shirin "Operation Gama Aiki."
An sake yin alkawarin kyautata ma 'yansanda a Najeriya
Yayin da ake cigaba da cecekuce kan karin farashin mai a Najeriya, wasu Hadiman Shugaban Najeriya da wasu magoya baya sun yi watsi da matsayin kungiyar kwadago, waddda ta ba da wa'adin tafiya yajin aiki.
A cigaba da bayyana ra'ayoyi da ake yi kan taron tsaro na yankin tafkin Chadi, wani kwararre ya ba da shawarar a rinka taron kowace shekara.
Yayin da ake ta musayar ra'ayi game da hanyoyin yakar Boko Haram, kwararru na ta bayyana muhimmancin wannan taron
Yayin da mata ke cigaba da taka rawa a sassan duniya daban-daban, yau duniya ta yaba masu.
Yayin da ake shiga lokacin tsananin zafi a Janhuriyar, ana kuma fama da karancin wutar lantarki
Batun binciken jami'an gwamnatin Bauchi da ta shude ya shiga wani sabon mataki ta yadda kwamitin binciken ya shawarci gwamnatin Bauchi ta APC da ta sa tsohon gwamna Isa Yuguda ya amayo Naira biliyan 80
Yayin da birnin Yamai na Janhuriyar Nijar ke bunkasa, an fara sa wando guda tsakanin gwamnati da kungiyar dillalan filaye musamman a birnin Yamai.
Shugaba Buhari na cigaba da samun yabo daga wadanda su ka san bala'in Boko Haram, musamman 'yan gudun hijira.
An lura cewa wata hanyar kare mutane daga cututtuka masu yawa ita ce tabbatar da tsafta, da lafiya da kuma ingancin ruwanda su ke sha.
Kamar kowace shekara, wannan shekarar ma ma'aikata a fadin duniya sun bayyana korafe-korafensu a wannan rana ta ma'aikata ta yau.
Yayin da ake ta kiraye-kirayen a taimaka ma masu fama a jahar Baorno, matar gawamnan jahar ta bayyana cewa ta kai dauki ma mabukata ne saboda ganin irin halin da su ke ciki na ban tausayi.
Jam'iyyar PDP ta sake fuskantar cikas bayan da wani jigonta, tsohon gwamnan jahar Bauchi, Isa Yududa, ya fice daga jam'iyyar kamar yadda wasu su ka yi a baya.
Yayin da ake ci gaba da samun rahotannin da ke nuna cewa ana samun galaba kan 'yan Boko Haram, sojojin Najeriya sun ba da rahoto kama wasu jagororin 'yan bindigar.
Domin Kari