An samu bullar wani al'amari da wasu ke cewa aljani ne tsaknin wasu dalibai mata a birnin Konni na Janhuriyar Nijar
Yayin da bangarori daban-daban a Janhuriyar Nijar ke ba da gudun mowarsu kan yadda za a ciyar da kasa gaba, su ma mabiya addinin gargajiya sun yi taro inda su ka bayar da tasu gudunmowar.
Yayin da aske ke dada zuwa gaban goshi, yakin nemar zaben na shugabancin Amurka na dada zafafa.
Gwamnatin Najeriya ta tashi haikan wajen karfafa gwiwar 'yan gudun hijirar Boko Haram da ke komawa gidajensu da su ka gudu su ka bari.
Ga dukkan alamu Shugaba Issouffou Mahammadou ya fara tauna tsakuwa dangane da masu cin hanci da rashawa a kasar. Mai yiwuwa ya gadar da kasa marar cin hanci kamar yadda ya yi alkawari
Matakin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauka na farfado da darajar Naira ta wajen cimma yarjajjeniyar musanyar Naira da takardar kudin China na samun yabo amma fa...
A cikin tattaunawar da aka yi akan yawan barkewar gobara a kasuwannin arewa masu muhawara sun bayyana dalilai da dama da suke haddasa gobara cikinsu har da sakacin 'yan kasuwan da wutar lantarki
Yayin da ake ta samun rigingimu tsakanin Fulani da manoma, wata kungiyar Fulani ta yi hobbasa wajen ganin abin ya zama tarihi
Ga dukkan alamau an kawo karshen takaddama da kuma jita-jita game da makomar kasafin kudin Najeriya na wannan shekarar, bayan da Kwamitin Kudi na Majalisar ya tabbatar da shiga zango na karshe na tabbatar da shi.
Yayin da ake samun karin bayani kan hare-haren da aka kai wani kauyen Gerei kwanan nan,
Rigimar cikin gidan jam'iyyar PDP ya fa dau wani sabon salo, bayan da wani jigon jam'iyyar daga arewa maso gabashin kasar ya mamaye Sakatariyar jam'iyyar ya ayyana kansa a matsayin sabon Ciyaman.
Yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin Buhari ya dau wani sabon salo bayan da 'yan jam'iyyarsa ta APC su ka kuduri aniyar kare manufofinsa mai shan suka daga bangaren PDP mai adawa.
Yayin da ake duba hanyoyin tallafa ma tattalin Najeriya, an lura cewa kayan jabu da ke fitowa daga China da sauran ire-irenta na kara yin illa ga tattalin arzikin kasar.
A wata hobbasa a yakin da ake yi da kungiyar Boko Haram da ke Najeriya, waddda kan ketare kan iyaka ta kai hare-hare a makwabtan kasashe, kasar Faransa ta agaza ma Kamaru da kayan yaki.
Za a kwadaita ma yara zuwa makaranta a jahar Kaduna ta wajen ciyar da su kyauta a makarantun Firamare, baya ga taimaka ma iyayensu da ciyarwar.
A cigaba da ketara kan iyakokin makwabtan kasashe su na aika-aika, 'yan bindigar Boko Haram sun wasu hare-hare a Kamaru. Na baya bayan nan shi ne na kunar bakin wake a wani masallaci.
Rahotanni na nuna 'yan Boko Haram sun shiga sace-sace musamman ma ma Fulani makiyaya, wanda hakan ke nuna wani sabon yanayi game da makomarsu
Yayin da ake cigaba da tunawa da Sardaunan Sakkwato, an ba da shawarar a yi aiki da misalolin da ya bari na alheri a baya.
Ga dukkan alamu ba a gama jin manyan labarai ba dangane da wasan koran da aka yi da kudaden da aka ware don sayo makaman yaki da Boko Haram.
Rundunar 'Yansandan Jahar Naija ta tabbatar da bugawar da PDP da APC su ka yi a garin Suleja, inda har aka samu raunuka.
Domin Kari