Yayin da bangarori daban-daban a Najeriya ke kokarin inganta kansu, su ma sojojin Najeriya sun tashi haikan wajen kare mutuncinsu. Na baya-bayan nan shi ne yakin da su ka kuduri aniyar yi da masu magudin zabe.
Ga dukkan alamu zazzabin lasa na cigaba da lakume rayuka a sassan Najeriya. Wannan kuma bai rasa nasaba da rashin fadakar da jama'a game da illar nau'in berayen da ke yada zazzabin
Yayin da yaki da mahandaman kudaden tabbatar da tsaron Najeriya ke kara zafafa, 'yan Majalisar Tarayyar Najeriya sun bayyana aniyarsu ta goyon bayan Shugaban a cewar wani shugaban kwamiti.
A cigaba da fadi-tashin da ake yi na ganin an farfado da tattalin arzikin kasashe daban-daban wadanda faduwar farashin mai ya shafe su, jami'an Hukumar Bayar Da Lamuni Ta Duniya (IMF) za su yi tozali da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Yayin da jahar Taraba ke fama da takaddamar siyasa, sai gashi kuma wata matsala ta satar mutane ta addabi kudancin jahar.
Duk da shakkun da wasu 'yan Najeriya ke nuna game da barin maharba su fafata da 'yan Boko Haram, maharban sun sake gabatar da bukatarsu ta a barsu su buga da 'yan bindigar.
'Yan sanda a jahar Bauchi sun yi awon gaba da shugaban kungiyar rajin yaki da satar dukiyar al'umma a Bauchi
Ana cigaba da samun kungiyoyi masu ba da gudunmowa a kokarin da ake wajen kare matasa daga masu cusa masu tsauraran ra'ayoyi
Da alamar an fara kai dauki ga wadanda harin da aka kai Madagali ya rutsa da su.
Sojojin ruwan Najeriya sun shiga sahun yaki da dumamar yanayi. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da ake ta yekuwa a fadin duniya kan barazanar dumamar yanayi
Shekaru hudu bayan kafa matatar man Nijar na SORAZ (La Société de raffinage de Zinder) da ke Damagaram, 'yan kasar na cewa ba su amfana.
Sabon tsarin tasi na zamani da aka bullo da shi a Kaduna na burge masu lura da al'akuran yau da kullum amma kuma tare da janyo ayar tambaya.
Wasu masu lura da al'amuran yau da kullum sun fara sukar abin da su ke kira yawan tafiye-tafiyen Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, duk da ya ke sun kuma ce ya na bukatar ya ziyarci wasu kasashe loto-loto
Jam'iyyar CPDM mai mulkin kasar Kamaru ta fara shirye-shiryen zabukan 2018 tun daga yanzu, ta wajen zaben sabbin shugabanni.
Rigimar jam'iyyar APC a jahar Gombe na kara sukurkucewa sakamakon irin hukuncin da kotu ta yanke bayan soke zaben Dan Majalisar Wakilai da kuma irin fassarar da ake ma hukuncin
An hori jami'an tsaron da za a tura ofisoshin jakadancin Najeriya da ke kasashen waje da su kasance masu kare kasarsu cikin ayyukansu.
Majiyoyi da dama na nuna cewa dan takarar gwamnan jahar Kogi na jam'iyyar APC ya rasu. Amma jam'iyyarsa ta APC ta sha gaba a tasoshin zabe da dama a Kogi.
Yayin da 'yan Boko Haram ke cigaba da kai munanan hare-hare har ma da kwace shanu da sauran dokiyoyi, wasu malaman addinin Musulunci a Lagos sun yi addu'ar Allah ya kawo kwanciyar hankali
Yayin da al'adar aibata juna ke wanzuwa tsakanin al'ummar Janhuriuyar Nijar, lauyoyin kasar sun gargadi jama'a da su daina.
An shiga turka-turka saboda albashi. Yayin da gwamnonin jahohi ke kare aniyarsu ta kin biyan Naira dubu 18 a matsayin albashi mafi karanci, su kuma kungiyoyin NLC da PDP da APC cewa su ke hakan zai saba ma doka.
Domin Kari