Batun kwarmata bayanan sirrin Amurka da wani tsohon ma'aikacin kwantaragi mai suna Edward Snowden ya yi ya dau wani sabon salo, bayan da aka ce Rasha da China sun leka cikin kudin bayanan sirrin da Snowden ya sacen
Yayin da dangantaka tsakanin Amurka da Rasha ke kara tsami, Amurka na duba yiwuwar jibge wasu manyan makaman yakinta a Turai da Baltic don tauna tsakuwa
Shugaban Amurka Barack Obama da sauran manya sun jinjina ma marigayi dan Mataimakin Shugaban Amurka Beau Biden.
Yayin da zaben Shugabannin Majalisar Tarayyar Najeriya ke kara karatowa, an kasa cimma jituwa kan fito da dantakarar Shugabancin Majalisar Dattawa na APC a bisa fahimta.
Ga dukkan alamu jam'iyyar APC ta kai ga cimma jituwa kan rage yawan 'yan takarar nemar kujerar Shugaban Majalisar Dattawa
Ta na kara bayyana cewa hukumar yaki da safarar muggan kwayoyi ta kama jigon PDP Kashamu Buruji ne saboda zargin harkar muggan kwayoyi a Amurka.
Sake aikata laifin kisa ya sa an sake shiga takaddama kan halaccin kariyar da kungiyoyin sa kai masu dauke da makamai ke yi
Jami'an tsaro sun janye daga Majalisar Dokokin jihar Naija har Majalisar ta yi zamanta na farko karkashin sabbin shugabanni
Yayin da ake dosar lokacin mika mulki ga gwamnati mai jiran gado, a jihar Kaduna an shiga gardama kan inda Kakakin Majalisar Dokokin jihar zai fito.
Bukin cikar kasar Afirka Ta Kudu shekaru 21 da kafa dimokaradiyya ya zo da caccakar kasashen Afirkan da mutanensu ke dunguma zuwa Afirka Ta Kudu
Rashin ware kudaden tallafin man fetur a kasafin kudin Najeriya na bana da kuma kudurin Shugaban Najeriya mai jiran gado ya yi na binciken dala biliyan 20 da ya bace, sun zama abin zance a Najeriya
Kawar da cutar maleriya za ta dau lokaci muddun jama'a ba su bayar da tasu gudunmowa kamar tsabtace muhalli da kau da kwantaccen ruwa ba, a cewar wani likita.
'Yar takarar gwamnan jihar Taraba ta jam'iyyar APC Hajiya A'ishatu Jummai Alhassan ta bayyana dalilanta na kin amincewa da sakamakon zaben jihar Taraba, wanda PDP ta ci
Yayin da duk wata kurar zabe ke kan kwantawa, yankunan Arewa Maso Gabas Da Arewa Maso Tsakiya sun shiga kokuwar shugabanci a Majalisar Tarayyar Najeriya mai zuwa.
An lura cewa idan bangaren zartaswa ya bar bangaren dokoki ya yi aikinsa, to za a samu cigaba sosai.
Gwamnonin Kano da Jigawa za su cigaba da ayyukan da gwamnonin yanzu su ke yi inbanda abin da ba a rasa ba
Wasu a cikin taron jama'a sun barke da ihu bayan da hukumar zaben Najeriya ta ba da satifiket din cin zaben Majalisar Wakilai ga wanda bai tsaya zabe ba
Yayin da ake dosar lokacin nade-nade a sabuwar gwamnatin APC ta jihar Adamawa, 'yan bangaren Atiku da Nyako sun fara karce kasa.
Ganin yadda matakan tsaro ke inganta a kan iyakokin Janhuriyar Nijar, Ministan Cikin Gidan kasar ya yaba da 'yan kasar musamman ma 'yan Maradi
Hajiya A'isha Buhari, matar Shugaban Najeriya mai jiran gado, ta ce duk mai tunanin wai za su rika kwasar kudaden gwamnati su na kyauta to su canza tunani
Domin Kari