Maharba na cikin ‘yan sa kai da suka taka muhimmiyar rawa na yaki da masu tayar da kayar baya na boko haram.
An kammala tantance maaikata da ‘yan fansho a jihar Bauchi amma kuma tantancewar ya bar baya da kura.
Jamiaan tsaro a kasar Kamaru suna tsare da wasu yara ‘yan mata biyu wadda daya daga cikin su tace tana cikin ‘yan matan nan na chibok da boko haram ta sace a cikin shekarar 2014.
Gobarar ta babbar kasuwar Birnin Kebbi babban birni jihar Kebbi ta soma ne tun da musalin karfe daya na dare inda ta dauki tsawon saoi da dama tana ci lamarin da ya shafi akasarin kasuwar baki daya.
Da musalin karfe 12 ne dai na dare gobarar ta tashi .
Wakiliyar Sashen Hausa daga Damagaran Tamar Abari ta aiko da rahoton cewa yankin Damagaran basu fito wurin zaben ba kamar yadda suka fito a zagayen farko. A cikin rahoton ga abinda take cewa.
A yau ne ake sake zabe zagaye na biyu a jamhuriyar Benin kuma Sahabu Imam Aliyu ya samu damar tattaunawa da wani dan kasuwa kuma dan siyasa Alhaji Amadu Cotounou.
Wakilin sahen Hausa daga Maradi Shaibu Mani ya jiwo daga bakin wasu masu jefa kuria kuma wasun su sun yaba wasu kuma sun soki zaben.
Zaben na watan 20 ga watan maris na da matukar muhimmaci ga ‘yan kasar Niger, domin a wannanzaben ne zasu zabi mutumin zai mulki kasar na tsawon waadi shekaru biyar masu zuwa.
A cewar shaidun gani da ido sunce matashin ya dauko shinkafa ne daga jamhuriyar Niger inda ya tsallako ta kan iyakar Illela amma kuma jamiaan kwastan suka tsare shi a wani shingen binciken su dake asara dake cikin karamar hukumar mulki ta Gwadabawa.
Taron wanda ake kira da faransanci Sesan Deluwa a bisa al’ada yakan baiwa ‘yan majilisar dokokin kasar Niger damar su nazarci kudurorin doka a bisa bukatar bangaren zartarwa inda ake shafe a kalla wattani biyu ana tafka muhawara.
Karancin man fetur naci gaba da kunno kai a birnin Abuja, inda ake ganin dogayen layuka a gidajen mai, dake ciki da wajen birnin
Daya daga cikin abubuwa da za taimaka musu dashi sun hada da Babura masu taya ukku.
Shugaba Buhari bai amsa ya zama cikakken dan demokaradiyya ba wajen rashin taya ni murnan lashe zabe.
Hukumar Zabe ta Najeriya a jihar Gombe ta haramta wa babban jamiyyar adawa APC a jihar tsayawa takarar dan majilisar wakilai ta tarayya ta mazabar Kumo wanda za’a yi yau laraba.
A yau laraba ne za’a rantsad da sabon gwamnan jihar Kogi dake tarayyar Najeriya Alhaji Yahaya Bello
Rahotanni sun tabbatar da cewa adadin wadanda suka kamu dama wadanda suka mutu sakamakon cutar ta Lassa sun karu a jihar Taraban.
A taron manema labarai da Musulman suka kira a , Mallam Dahiru Bauci ya tattauna da wakilin sashen Hausa Abduwahab Muhammed kan wannan batu.
Shugaban hukumar yace abin takaici ne ma’yan gudun hijirar sun shafe fiye da shekara guda amma babu taimakon kuzo ku gani da gwamnatin jihar ke basu.
An tattauna akan abubuwa da yawa musammam akan maganar harkan tsaro,wanda shugaba Muhammadu Buhari baiyi nauyin bakin na neman taimako na wannan kasar wadda take da arziki a duniya domin taimakawa da yaki da akeyi da taaddanci da kuma a taimakawa jama’an da suka galabaita sakamakon wannan yaki.
Domin Kari