Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sam ba za ta karba gayyatar gwamnatin tarayya na zaman sasantawa da kungiyar kwadago ba.
Tsohon shugaban Najeriya na mulkin soji Janar Ibrahim Badmasi Babangida, ya bayyana yakinin cewa za’a iya shawo kan matsalar tsaro da ke addabar dukkan sassan kasar ne kadai, idan aka sami kishin kasa da fahimta tsakanin gwamnati da ‘yan kasa.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bukaci da a gaggauta cire Ministan sufuri na kasar Rotimi Amaechi, sakamakon zarge-zargen sama da fadi da naira biliyan 165 na hukumar tashoshin ruwan kasar.
Za'a soma duban jinjirin watan Shawwal a ranar Talata a Najeriya, yayin da shugaba Muhammadu Buhari zai gudanar da sallar idi a fadar shugaban kasa, tare da bin ka'idojin yaki da cutar coronavirus.
Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta maida martani akan ikirarin fadar shugaban kasa, cewa wasu ‘yan kasar na kokarin kifar da gwamnati ta hanyar da ta sabawa tsarin dimokaradiyya.
Gwamnatin jihar Bauchi ta ankarar da jama’ar jihar cewa ana zargin ‘yan kungiyar Boko Haram suna kwararowa daga Geidam ta jihar Yobe zuwa cikin jihar.
Rundunar sojin Najeriya ta maida martani akan kiraye-kirayen da ake yi na cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya mika mata mulkin kasar domin ceto ta daga wargajewa.
Rahotanni daga jihar Zamfara na bayyana cewa an kashe biyu daga cikin manyan shugabannin ‘yan bindigar da suka addabi jama’a a jihohin Zamfara da Katsina.
Yanayin tabarbarewar tsaro a dukkan sassan Najeriya ya sa majalisar wakilan kasar ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya ayyana dokar ta baci akan sha’anin tsaro a kasar.
Wasu mutane da ake zargin mayakan kungiyar nan ce mai fafutukar kafa kasar Biafra - IPOB, sun kai farmaki ga wata al’ummar Fulani a jihar Anambra, inda suka kashe akalla mutum 19.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana gana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken, inda suka tattauna kan batutuwan da suka hada da karfafa dangantakar kasashen biyu da kuma batun tsaro.
Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra wato IPOB ta ce ta nada sabon shugaba, wanda zai maye gurbin babban kwamandanta da jami’an tsaro suka kashe a jihar Imo.
Allah ya yi wa Hajiya Maryam Ado Bayero matar tsohon sarkin Kano marigayi Ado Bayero kuma mahaifiyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero rasuwa.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta sami nasarar dakile wani harin 'yan kungiyar Boko Haram, ta hanyar amfani da jiragen yaki, inda suka fatattaki mayakan a garin Geidam da ke jihar Yobe.
A karshe dai shahararren malamin addinin Musulunci a Kaduna Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana dalilin dakatar da rangadin jagorancin sulhu tsakanin ‘yan bindiga da gwamnati da ya soma a kwanakin baya.
Majalisar dattawan Najeriya ta amince da bukatar da gwamnatin tarayyar kasar karkashin jagorancin shugaba Muhammadu ta gabatar mata a cikin watan Mayun shekarar 2020, na neman rancen dala biliyan biyu da miliyan 700 cikin dala biliyan biyar da miliyan 500 daga waje.
Rahotanni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa an gudanar da jana'izar gomman mutanen da 'yan bindiga suka hallaka, bayan wani mummunan hari da suka kai a wasu kauyuka 4 a ranar Laraba.
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali ya ba da umarnin janye dukan manyan jami’an ‘yan sandan da ke hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ba tare da bata lokaci ba.
Kotun sauraren karar zaben gwamnan jihar Ondo, ta tabbatar da sake zaben gwamnan jihar Rotimi Akeredolu na jam’iyyar APC, inda ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP Eyitayo Jegede ya shigar yana kalubalantar zaben.
An yankewa tsohon jami’in ‘yan sanda farar fata, Derek Chauvin, hukunci akan kisan Ba’amurke bakar fata George Floyd, a yayin da yake kokarin kama shi a birnin Minneapolis.
Domin Kari