Dazu dazunnan ne shugaban kasar Kamaru Poul Biya, ya sauka a babban birnin Najeriya Abuja, domin fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu a makwabciyar kasar.
'Yan fashin teku a kasashen Yammacin Afrika sun koma garkuwa da mutane, yayin da mayakan ruwan yankin suke kara kaimi wajen shawo kansu, bisa ga wani rahoton da wata kungiyar yaki da ‘yan fashin teku ta fitar yau Talata.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya yace gwamnatin da ta gabata ta sace Dala Miliyan Dubu Goma sha Biyar na talakawa ta wajen badakalar sayen makamai.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 3 ga watan Mayu domin bukin ranar yancin yan jaridu, taken bukin bana dai shine samar da yanci na yada labarai a matsayin daya daga cikin yacin bil Adama da kuma kare yan jaridu wajen gudanar da ayyukansu ba tare da sa musu tukunkumi ba, da kuma tabbatar da lafiyarsu.
Neman karin mafi karancin albashi da kungiyoyin kwadagon Najeriya sukayi a ranar ma’aikata ta bana da alamu bai samu kwakkwarar amsa daga gwamnatin da ke famar karbar kasafin kudi, daga Majalisa da nufin fara wasu ayyuka da masu zabe zasu fara shaidawa.
Har ya zuwa yanzu dai dokar da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-Rufa’i ya kaiwa majalisar dokokin jihar game da yadda Mallaman addinin Krista da Musulmi zasu gudanar da wa’azi tana gaban Majalisar.
Dakarun kasar Turkiya sun halaka mayakan ISIL 63 a Syria, bayan da suka kai wani farmaki daga filin tashin jiragen dakarun kasar da ke Incirlik, kamar yadda wata sanarwa da sojojin kasar suka fitar ta nuna.
Rundunar sojan Najeriya shiyya ta bakwai dake garin Maiduguri tace ta samu nasarar kawar da wani harin wasu yan kungiyar kunar bakin wake mata 4 da ake kyautata tsammanin sun fito ne daga dajin Sambisa, kuma sun tunkari wani kauye da ake kira JImini Bolori.
Gwamnatin Najeriya ta mayar da martani ga matasan nan dake shirye shiryen mamaye fadar shugaban kasa ta Aso Rock don kokawa bisa wahalhalun rayuwa da talakawan kasar ke fuskanta.
Duk da yake kowanne dan kasa na da ‘yancin fita domin neman waraka daga cutar dake damunsa, babban abin takaici inji shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, a ta bakin ministan lafiya, shine yadda yan kasar ke yin tururuwa a kasashen waje domin neman maganin rashin lafiya.
Majalisar Dokokin jihar Bauchi ta baiwa babban akanta janar na jihar wa’adin mako guda daya biya dukkan ma’aikatan jihar da aka kammala aikin tantancesu albashi.
Cikin watan Maris ne a cibiyar yaki da Boko Haram dake Maiduguri, kwamandan rudunar Zaman Lafiya Dole, Manjo Janar Leo Irabor, ya bayar da kwarin gwiwar karya lagon ‘yan ta’adda da nuna cewa za a kawo karshensu nan bada dadewa ba.
Tsohon hafsan rundunar sojan saman Najeriya, Aliko El-Rashid Harun, wanda kwararre ne kan sha’anin tsaro yace akan shigo da makamai ga yan Boko Haram cikin Najeriya ta kan iyakokin kasar, wanda ke da yawan gaske kuma ba a saka musu idanu.
Wasu daga cikin yan jihar Kaduna da shugabannin al’umma na ci gaba da korafe korafe game da wasu daga cikin dokokin da gwamna mallam Nasiru El-Rufa’in jihar Kaduna yakai gaban Majalisa.
Wandansu mutane da ba a san ko suwaye ba sun kai hari a yammacin jiya, a wani kauye da ake kira Egrak, dake cikin jihar Tawa a kasar jamhuriyar NIjar.
Ana kyautata zaton shahararren dan kwallon nan na Liberia George Weah, wanda ke jam'iyyar adawa ta CDC, zai yi na'am da bukatar magoya bayansa cewa ya shiga takarar zaben Shugabnan kasa na shekara ta 2017.
Kasar Koriya Ta Kudu ta ce 'yan wasanta na Olympic za su sa riguna masu dogayen hannu da kuma wanduna masu dauke da sinadaran korar sauro a yayin shagulgula da kuma atisayen gasar Olympic ta 2016 da za a yi a birnin Rio de Janeiro.
Domin Kari