Zaben na shugban kasa da ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a fadin Najeriya, an gudanar lami lafiya a fadin Jahar Filato, in banda matsalolin rashin kai kayan aiki da wuri a wasu rumfunan zabe, lamarin da ya haifar da rashin fara zaben a kan lokaci.