Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Masu Zanga-zanga A Jihar Filato Na Zargin Jami’an Sojoji Da Kisa


Wasu Mata Da Suka Yi Zanga-zanga A Garin Mangu Na Jihar Filato
Wasu Mata Da Suka Yi Zanga-zanga A Garin Mangu Na Jihar Filato

Wassu mata da suka yi zanga-zanga jiya Litinin a garin Mangu na jihar Filato, da ke fama da tashin hankali sun zargi jami’an soji da wuce gona da iri, da kashe wani matashi.

JOS, NIGERIA - Zanga-zangar da matan suka yi ta biyo bayan kisan wasu mutane ne da ‘yan bindiga suka yi a kauyen Chia, inda suka kashe mutane hudu, ciki har da mace mai ciki, lamarin da matan su ka ce sojojin basu dauki matakin hana kisan ba.

Matan sun bayyana cewa yayin da suka fita zanga-zangar sun tare hanya sai sojojin suka harbe wani matashi da wasu mata, inda nan take matashin ya mutu, matan kuma suna asibiti.

Zamga-zanga a garin Mangu na Jihar Filato
Zamga-zanga a garin Mangu na Jihar Filato

Sun kuma kara da cewa basu bukatar sojoji a yankin.

Komared Jerry Datim dake aiki da kungiyar Human Rights Watch ya ce kisan mutane hudun da ‘yan bindigar suka yi a kauyensa ne amma duk da shike ya kira dakarun, basu kai dauki cikin gaggawa ba.

A gefe guda kuwa, kakakin rundunar dake aikin samar da tsaro a jihar Filato, Keftin John Oya ya ce matan sun yi yunkurin kona shelkwatar rundunar ne, da ke Mangu, a kokarin hana su shi ne jami’an sojin suka yi harbi, bisa tsautsayi ya kashe matashin amma ba da nufin kisa ba.

Keftin Oya ya ce ba gaskiya bane cewa sojoji sun daki wasu mata, inda ya kara da cewa tun makonni uku da dakarun suka fara aiki a Mangu an sami zaman lafiya da ya kamata a yaba musu.

Lokacin wata zanga-zanga da mata suka yi a garin mangu na jihar Filato
Lokacin wata zanga-zanga da mata suka yi a garin mangu na jihar Filato

Kakakin na STF ya ce sun cafke mutane biyu da suke zargi da kashe mutane hudu a kauyen na Chia.

A halin da ake ciki kuma kungiyar matasan Kabilar Berom ta yi Allah wadai da kisan da aka yi wa wani mutum, da wasu dake dauke da makamai cikin dare suka tare wata mota da ta fito daga kasuwar kara a garin Bukur.

Kungiyar a wata sanarwa da sanya hannun kakakinta, Rwang Tengwong ta yi fatan irin wannan lamari ba zai sake faruwa ba, yayin da tace ana gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata danyen aikin.

Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:

NIGERIA: Masu Zanga-zanga A Jihar Filato Suna Zargin Jami’an Sojoji Da Kisa.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG