Hukumomi a kasar Argentina sun fada a jiya Asabar cewa, birnin Bahia Blanca mai tashar jiragen ruwa ya lalace sakamakon ruwan sama da ya kai na shekara guda a cikin sa'o'i kadan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13 tare da fidda daruruwan mutane daga gidajensu.
A makon da ya gabata, Isra’ila ta matsawa Hamas lamba da ta sako ragowar mutanen da take garkuwa da su na karin lokaci a fuskar yarjejeniyar ta farko, wadda ta kare a karshen makon jiya da kuma daukar alkawarin shiga tattaunawar karshe.
Dubban Mata ne suka gudanar da zanga-zanga a titunan biranen kasar Turkiyya, domin tunawa da ranar mata ta duniya, inda suka nuna adawa da rashin daidaito da cin zarafin Mata.
A yau Laraba, Afrika ta Kudu tayi tir da takaita shigar da kayan agaji zuwa zirin Gaza da yaki ya daidaita da Isra'ila ke yi tun a karshen makon da ya gabata, inda tace hakan tamkar amfani da yunwa ne a matsayin makamin yaki.
Akalla mutum 12, ciki har da mata da kananan yara ne suka mutu a wani tagwayen harin kunar bakin wake da aka kai ranar Talata, a wani yanki da ke arewa maso yammacin Pakistan.
A yau Talata, Shugaba Volodymyr Zelensky ya bayyana cewar yana bukatar daidaita al'amura tsakaninsa da Donald Trump tare da yin aiki karkashin jagorancinsa domin samar da dawammen zaman lafiya a ukraine.
Sheinbaum ta kuma zargi Washington da wallafa sanarwar batanci da bata mata suna ba tare da wata hujja ba
Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.
A ranar Asabar ne kashin farko na yarjejeniyar tsagaita wutar ya kare, inda kungiyar mayakan Hamasa da Isra’ila da Amurka suka ayyana da kungiyar ta’addanci ke tababar yadda kashi na biyu na yarjejeniyar zai kasance.
Ministocin sun gudanar da taron share fagge da tuntubar juna da mayar da hankali a kan sake gina zirin da yaki ya daidaita ba tare da raba mazauna cikinsa su miliyan 2.4 da matsugunansu ba.
Yarjejeniyar wacce ya kamata ta zama matakin da zai taimaka wajen kawo karshen yakin Ukraine ta cije bayan wata arangama da Shugaba Donald Trump na Amurka a fadarsa
Shirin fim mai taken “No Other Land,” labarin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da ke fafutukar kare al’ummomin su daga yunkurin rushe su da sojoji Isira’ila ke yi, ya lashe kyautar Oscar ta fitaccen shiri na musamman a ranar Lahadi.
Domin Kari