Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa ga Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama da Sha'anin Sararin samaniya, Tunde Moshood, ya sanya wa hannu a ranar Laraba.
Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya karbi bakuncin jakadan Jamaica a Najeriya, Lincoln Downer, da Jami'in karamin ofishinsa, Andre Hibbert, zuwa ofishinsa da ke Abuja domin gudanar da wannan aiki.
Downer ya jaddada yuwuwar kulla huldar diflomasiyya yadda za a ci moriyar juna tsakanin kasarsa ta Jamaica da Najeriya.
Ya bayyana mahimmancin samun ci gaba da inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, ciki har da yin nazari kan yarjejeniyar da aka kulla a tsakanin kasashen biyu.
Downer ya ce " kasata ta dora min alhakin yin nazari tare da inganta huldar diflomasiyya tsakanin Jamaica da Najeriya, musamman kan harkokin sufurin jiragen sama."
Jakadan na Jamaica ya kuma bayyana yadda ake samun karuwar sha'awar al'adun Najeriya, musamman kidan Afrobeat da fina-finan Nollywood, wadanda ke yaduwa a kasar Jamaica. Wannan musayar al'adu, in ji shi, na kara karfafa bukatar inganta huldar diflomasiyya da ta sufuri.
“Babu dalilin da zai hana mu jirage masu zirga zirga kai tsaye tsakanin kasashenmu. 'Yan Najeriya na son Jamaica, kuma ana samun karuwar bukatar kayan kamshin Jamaica a Najeriya," in ji Downer.
Dandalin Mu Tattauna