Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Gwagwarmaya Na Ci Gaba Da Zanga Zanga A Islamabad


Masu Zanga Zanga a Islamabad

Sakamnakon zartas da hukuncin kisa kan mutumin da ya harbe wani gwamnan lardin kasar, wanda ya jagoranci yunkurin kwaskwarima ga dokokin da suke batanci ga addini.

A Pakistan an shiga rana ta hudu da daruruwan wasu ‘yan gwagwarmaya suna ci gaba da zanga-zanga a babban birnin kasar Islamabad, sakamnakon zartas da hukuncin kisa kan mutumin da ya harbe wani gwamnan lardin kasar, wanda ya jagoranci yunkurin kwaskwarima ga dokokin da suke batanci ga addini.

Magoya bayan Mumtaz Qadri wanda ya harbe Salman Taseer a cikin shekarar 2011 lokacin yana gwamnan daya daga cikin jihohin da suka fi tasiri a kasar, sunki su watse a harabar da suke gudanar da wannan zanga-zangar, suna cewa sai gwamnati ta basu tabbacin cewa ba zata canza dokar nan na kalaman batanci ga addini ba.

Haka nan kuma masu zanga-zangar sun bukaci gwamnati ta rataye matar nan kirista wadda gwamnan ya kekarewa daga kalaman batanci da tayi wa addini.

Yan sanda sun shirya tarwatsa yi kokarin tarwatsa masu zanga-zangar amma daya daga cikin su ya shaidawa kanfanin dillacin labarai na ASSOCIATED PRESS cewa a shirye yake ya sadaukar da ransa kan wanan batu.

Wannan zanga-zangar da ake yi kusa majilisar dokokin kasar ya haifar da tsaiko ga harkokin yau da kullun a wasu sassan Islamabad,ta kai ga mahukunta sun bada umurnin katse wayoyin wayar salula a ciki birnin tare da rufe wasu hanyoyi domin hana wasu shiga tawagar masu zanga-zanga

XS
SM
MD
LG