Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsamo Gawarwarkin Mutane Fiye da Dari daga Teku


Mutane ashirin da takwas ne kacal ake kyautata zaton sun tsira a lokacinda jirgin ya kife

Rundunar mayakan ruwan kasar Italiya a yau Laraba take ko kuma ta fiddo buraguzon jirgin ruwan daya nutse a watan Afrilun shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, da ake kyautata zaton a lokacinda nutse yana jigilar yan gudun hijira yan Afrika kimamin dari bakwai.

Yau zuwa yanzu dai mayakan ruwan sun samu nasarar zakulo fiye da gawarwarkin mutane dari, to amma mutane da dama ciki harda mata da yara, ana kyautata zaton suna ciki ko kuma karkashin jirgin.

A ranar sha takwas ga watan Afrilun shekara ta dubu biyu da goma sha biyar jirgin ruwan ya kife kimamin kilomita dari da tamanin da takwas kudu da tsibirin Lampedusa na kasar Italiya.

Mutane ashirin da takwas ne kacal ake kyautata zaton sun tsira a lokacinda jirgin ya kife bara. Wannan al’amari ya fusata jama’a da tilastawa kungiyar kasashen turai

kara goyon bayan aikin neman wadanda hatsarin jirgin ya rutsa dasu.

Jami’an kasar Italiya sunce a makon jiya sun ceci yan gudun hijira dubu bakwai.

XS
SM
MD
LG