Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bama Bamai Sun Tashi


Soldiers from the United Arab Emirates walk past a military vehicle at the airport of Yemen's southern port city of Aden, Aug. 12, 2015.
Soldiers from the United Arab Emirates walk past a military vehicle at the airport of Yemen's southern port city of Aden, Aug. 12, 2015.

Akalla an kashe mutane shidda a musayar harbe harbe

Kafofin soja a kasar Yamal sunce yau Laraban nan, ranar Sallah harin kuna bakin wake na bam da aka boye cikin motoci biyu sun kaiwa wani sansanin soja kusa da filin saukar jiragen saman birnin Aden hari.

Akalla mutane shidda aka kashe. Kafofin tsaro sun ce an yi musayar harbe harbe, kuma bama bamai sun tashi a yayinda yan yakin sa kai suka yi kokarin amfani da rudami da aka samu domin yin karin barna.

Birnin Aden yana zama hedikwatar gwamnatin Yamal na wucin gadi, tun lokacinda sojojin gwamnati suka sake kwace birnin a bara. To amma kuma munanan hare hare sun zama ruwan dare a birnin.

A watan Mayu, wasu masu harin kunar bakin wake na kungiyar ISIS sun kashe kuratan sojoji arba’in da biyar a sansanin sojan birnin Aden.

XS
SM
MD
LG