Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A BARI YA HUCE: Labarin Bafulllatani Da Saniya Mai Magana, 20, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

A wannan shirin mun bada labarain wani Bafulatani da ya tafi kiwo da karenshi, suna cikin jeji sai wata saniya ta ware ta tafi gona tana barna. Kamar yadda Fulani suka saba, sai ya yi kokarin kora ta ta koma sauran garke, ya rika dukanta da sanda ta ki matsawa, sai can an jima Saniya ta juya ta ce mashi, haba Malam kamar ka sami jaka? Da jin haka sai bafullatani ya wurgar da sanda ya kama gudu ya bar shanun a jeji. Ya yi ta gudu kamar ranshi zai fita. karenshi yana ta binshi da gudu. Da ya yi nisan gaske sai ya zauna ginjin wata bishiya yana haki. Da hankalinshi ya dawo sai ya ce. Kai, yau munga boni. Tunda nake ban taba jin dabba ta yi magana ba. Sai shi ma karan yace wallahi nima haka

Idan Kaine ya zaka yi?

Saurari cikaken shirin:

A Bari Ya Huce: Labarin Bafullatani Da Saniya Mai Magana-24: 00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:24:33 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG