Accessibility links

Tsohon mataimakin Sifeton janar din ‘yan sanda Senata Nuhu Aliyu

Tsohon mataimakin Sifeton janar din ‘yan sanda Senata Nuhu Aliyu, yace nauyin wayar da kan jama’a, akan addinin Musulunci ya rataya ne akan shuwagabani da malaman addini.

Ya furta haka ne a wani taron shekara –shekara da wani kwamitin fadakarwa game da addini musulunci da masarautar Kontagora a jihar Nejar ta kafa.

Yace hakan ya Zama wajibi domin yankan bata gari masu neman bata addinin Musulunci, yana mai cewa duk abunda ya faru kaji ance Boko Haram.

Yana mai kari da cewa rashin ilimi yana kawo illa ga aluma saboda haka ya gargadi jama’a da ayi da hankula.

Shima tsoho Gwamna jihar Kano Kanal Sani Bello maritaya yayi hanun ka mai sanda ne ga jama’a inda yake cewa yakamata a kula da irin bakin da ake bawa masauki.

Kwamitn ya samu nasarori da dama waje hada kan aluma inji Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Saidu na Maska, inda ya bukaci Karin hadin kan Malamai da Hakiman dake masarautar shi.
XS
SM
MD
LG