Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bam da aka boye cikin wata motar a kori kura ya fashe jiya Laraba da safe a unguwar da ofisoshin jakadanci suke a Kabul baban birnin kasar Afghanistan ya kashe akalla mutane casa’in da raunana fiye da mutane dari uku.

Wani Jami’in tsaro da yace a sakaya sunan sa, shi ya baiyanawa Muryar Amirka yawan mutane da suka mutu sa’o’i bayan tashin bam din.

Tunda farko mai magana da yawun ma’aikatar kiwon lafiya ta Afghanistan Wahidullah Majroh yace mutane tamanin ne suka mutu, kodayake yace akwai yiwuwar adadin ya karu.

Bam din ya ratsa yankin Wazir Akbar Khan na birnin Kabul inda nan ne ofisoshin jakadancin kasashe da ofisoshin gwamnati suke. Bam din ya lalata motoci da gine ginen da suke kusa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG