Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abin Da Ke Faruwa A Gaza Ba Kisan Kare Dangi Ba Ne – Biden


Shugaban Amurka President Joe Biden
Shugaban Amurka President Joe Biden

"Abin da ke faruwa a Gaza ba kisan kare dangi ba ne, mun yi watsi da hakan," in ji Biden a wani taron watan al'adun Yahudawa na Amurka a fadar White House.

Shugaban Amurka Joe Biden ya kare Isra'ila da kakkausar murya a jiya Litinin, yana mai cewa sojojin Isra'ila ba sa aikata kisan kiyashi a yakin da suke yi da mayakan Hamas a Gaza a wani mataki na yin watsi da sukar da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu suka yi.

Palestinians inspect the site of an Israeli strike on a house, in Nuseirat
Palestinians inspect the site of an Israeli strike on a house, in Nuseirat

"Abin da ke faruwa a Gaza ba kisan kare dangi ba ne, mun yi watsi da hakan," in ji Biden a wani taron watan al'adun Yahudawa na Amurka a fadar White House.

Biden ya fuskanci zanga-zanga a yawancin al'amuransa a fadin kasar daga masu fafutuka masu goyon bayan Falasdinu wadanda suka yi masa lakabi da "Joe mai kisan kare dangi" saboda tsayin daka na goyon bayansa ga Isra'ila.

People supporting Palestine, take part in a protest against Israel, in front of the Israeli Embassy in Washington, DC, on March 2, 2024.
People supporting Palestine, take part in a protest against Israel, in front of the Israeli Embassy in Washington, DC, on March 2, 2024.

A wani jawabi da ya yi a fadar White House, Biden ya jaddada imaninsa cewa Isra'ila ce aka zalunta tun a ranar 7 ga watan Oktoba da mayakan Hamas suka kai a kudancin Isra'ila inda suka kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da daruruwan mutane.

"Muna tare da Isra'ila don mu karasa (shugaban Hamas Yahya) Sinwar da sauran mahautan Hamas. Muna son mu ci nasara kan Hamas, muna aiki tare da Isra'ila don ganin hakan ta faru," in ji shi.

Biden ya kuma yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza, abin da ya sake nanata a jawabinsa na farko a Kwalejin Morehouse ranar Lahadi.

Biden Morehouse Commencement
Biden Morehouse Commencement

Biden ya kuma yi watsi da mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa kan cewa ya bukaci sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da babban jami'in tsaronsa kan zargin aikata laifukan yaki.

Mai shigar da kara na kotun ICC a ranar litinin ya kuma ce ya bukaci sammacin kama shugaban Hamas Sinwar da wasu shugabannin Hamas biyu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG