Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Wadanda Suka Kamu Da COVID-19 a Najeriya Ya Doshi 60,000


Ministan Lafiya Osagie Ehanire
Ministan Lafiya Osagie Ehanire

Hukumar NCDC mai kula da cututtuka masu yaduwa a Najeriya ta ce an samu karin mutum 120, da suka kamu da cutar COVID-19 a ranar Litinin, 05 ga watan Oktoba.

A bayanan da ta saka a shafinta na Twitter a daren ranar Litinin, hukumar ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ya kai 59,465 a kasar, yayin da jihar Rivers ta samu karin mutum 65.

Sauran wuraren sun hada da Birnin Tarayya Abuja, inda aka samu mutum 12, sai Ogun 9, Katsina 8 Anambra 7, Bauchi 5 Oyo 5, Nasarawa 3, Kaduna 2, Kwara 1, Taraba 1, Imo 1, Delta 1.

Gaba dayan adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar yanzu ya kai 59,465, an kuma sallami mutum 50,951, sannan mutum 1,113 ne suka mutu.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG