Accessibility links

Adadin Wadanda Suka Mutu Da Cutar Ebola A Kasar Kwango Ya Karu


Wani fada ya ziyarci cibiyar jinyar masu cutar Ebola

An sake samun wani da ya mutu da cutar Ebola a Congo, abinda ya kai adadin wadanda cutar ta kashe zuwa goma sha biyu, bisa ga cewar ma’aikatar lafiya ta Damokaradiyar Jamhuriyar Kwango.

Rasuwar ta auku ne a kauyen Iboko dake arewa maso yammacin lardin Equater.

Ma’aikatar lafiya tace akwai kuma wadansu mutane hudu da ake kyautata zaton sun kamu da cutar a lardin. Yanzu haka an tabbatar mutane talatin da biyar sun kamu da cutar ta Ebola a kasar Kwango.

Gobe litinin za a fara allurer rigakafin cutar Ebola a kauyukan Bikoro da Iboko dake lardin Equateur. Ana kuma shirin rigakafi a Mbandaka, babban birnin lardin mai mutane miliyan daya da dubu dari biyu, dake bakin kogin Kwango, inda aka tabbatar da mutane hudu sun kamu da cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG