Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Lallasa Egypt A Wasanta Na Farko a Gasar AFCON


"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar

Shahararren dan wasan gaba na Liverpool Salah bai tabuka abin kirki ba, sakamakon yadda zaratan ‘yan wasan Najeriya suka rike shi tsawon mintuna 90 da aka yi a wasan.

Babban wasa na biyu da kowa ke jiran gani a gasar cin kofin Afrika na shekarar 2021 tsakanin Najeriya da Misra, ya zo karshen inda Najeriya ta yiwa Misra da shahararren dan wasanta Mohamed Salah ci daya mai ban haushi.

Bayan wasan Ghana da Morocco a jiya Litinin da ita ma Ghana ta sha ci daya da nema, wasan da aka kwatanta da karan batta da ake gani kowane bangare na iya daukar kofin, sakamakon wasan Najeriya ce ta yi shirin daukar kofin gasar Afrika ta bana.

Shahararren dan wasan gaba na Liverpool Salah bai tabuka abin kirki, sakamakon yanda zaratan ‘yan wasan Najeriya suka masa rike shi tsawon mintuna 90 da aka yi wasan.

Kwallon da Kelechi Iheanacho ya zura a zagayen farkon wasan ya baiwa Najeriya damar tattara maki uku na wasan.

Ana sa ran kungiyoyin wasan kasashen biyu za su yi fice daga rukunin D zuwa matsayi na gaba duk da sakamakon wasan na yau, amma nasarar da Super Eagles ya gayara mata hanyar isa ga zagayen da kasashe 16 zasu fafata kana ya bata kwarin gwiwa a wannan gasa, yayin da ita Misra take cikin damuwa a lokacin da take Shirin yin sauran wasanninta da Guinea-Bissau da Sudan.

Moses Simon na bangaren Najeriya, shi ne ya fi taka leda a wasan, duba da irin rawar gani da ya taka a gefen filin wasan.

Yanzu Najeriya za ta kara ne da Sudan a was anta nag aba wanda za a yi a ranar Asabar.

Ita kuwa Egypt za ta kara ne Guinea Bissau a ranar ta Asabar duka a rukuninsu na D.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG