Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Kai Zagayen ‘Yan 16 A Gasar AFCON


'Yan Najeriya masu ta da tsumin goyon baya a Kamaru
'Yan Najeriya masu ta da tsumin goyon baya a Kamaru

A ranar Laraba Najeriya za ta kara da Guinea-Bissau duk da cewa ta shiga zagaye na gaba yayin da Sudan za ta fafata da Masar.

Najeriya ta samu gurbin shiga zagayen ‘yan 16 bayan da ta doke Sudan a wasanta na biyu a gasar cin kofin nahiyar da ake yi a Kamaru a rukunin D a garin Garoua.

‘Yan wasan na Super Eagles sun doke Sudan da ci 3-1 inda Samuel Chukwueze ya yi sammakon zura kwallon farko a minti na uku da fara wasa.

Kwallo ta biyu kuma ta zo ne daga Taiwo Awoniyi gab da za a tafi hutun rabin lokaci, wato a minti na 45.

Bayan kuma da aka dawo daga hutun rabin lokacin ne Moses Simon shi ma ya ba da tashi gudunmowar kwallon a minti na 46.

Sai dai a minti na 70 Sudan ta samu bugun fenariti wacce Khedr Safour Daiyeen ya buga ya ci.

Duk da cewa sun zubar da dama da yawa a karawar, Najeriya ta yi hobbasan ganin ta mallaki gurbi a zagayen da za a fara sallamar kasashe zuwa gida.

Najeriya ta lallasa Masar a wasanta na farko inda ta doke tawagar dan wasan Liverpool Mohamed Salah da ci daya mai ban haushi.

Sau uku Najeriya tana lashe kofin na AFCON, lokaci na baya-bayan nan shi ne a shekarar 2013.

Ita kuwa Sudan ta taba lashe kofin gasar a shekarar 1970 kuma shekararta goma rabon da ta halarci gasar ta AFCON sai a wannan karo.

A wasanta na farko, Sudan ta tashi kunnen doki da Guinea-Bissau a wasanta na farko inda har golanta Ali Abu Achrine ya yi nasarar kakkabe wani bugun fenarti.

A ranar Laraba Najeriya za ta kara da Guinea-Bissau duk da cewa ta shiga zagaye na gaba yayin da Sudan za ta fafata da Masar.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG