Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aikin Rigakafi Na Fuskantar Cikas Musamman A Karkara


Yayin da aka samu bullar nau’in omicron na coronavirus, yin allurar rigakafi wa mutane da yawa don hana yaduwar sabon nau’in, na fuskantar kalubale kan hanyoyi a Najeriya. . Yanzu haka mutane miliyan 3.78 ne kawai ke da cikakken rigakafin.

Satar mutane a kan hanya da wasu gungun 'yan bindiga ke yi ya zama ruwan dare. Amma irin waɗannan tafiye-tafiye suna da mahimmanci idan ƙasar da ta fi yawan al'umma a Afirka tana son cimma burinta na yi wa mutane miliyan 55 cikakken allurar rigakafi daga cikin miliyan 206 a cikin watanni biyu masu zuwa.

A cibiyar lafiya ta Sabo da ke Kuje, wani gari mai mutane kusan 300,000 da ke kusa da filin jirgin sama na Abuja, Malam Bawa da wasu abokan aikinsa uku suna aiki a cikin gidajen da suka rugurguje da kayan ofis da suka lalace. A cikin watanni ukun da suka gabata, a biyu ne kawai suka samu biya daga gwamnati, inda suka samu kusan Naira 10,000 na Najeriya kwatankwacin dala 24.

A rana mai kyau, Bawa zai iya kai wa kusan mutane 20 rigakafin, amma yawanci biyar ko ƙasa da haka.

Wannan yakan haifar da cikas ga Bawa da abokan aikinsa, baya ga hadarin tashin hankali da jiran makonni don biyan hakki. Ya ce bai san lokacin da gwamnati za ta biya shi albashin nasa ba.

Kungiyoyin 'yan bindiga a yankin arewa maso yammacin Najeriya da tsakiyar Najeriya sun kashe daruruwan mutane a bana tare da yin garkuwa da dubbai, domin neman kudin fansa.

A wuraren da ba a cika samun tashin hankali ba, jinkirin biyan ma’aikatan da ke jigilar kayayyaki da bayar da allurar rigakafin ya kasance “babban kalubale ne a gare mu,” in ji Dokta Rilwanu Mohammed, babban jami’in gwamnati da ke jagorantar ayyukan rigakafin a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Jami’ai suna kuma yaki da shakku game da allurar rigakafin a sassa da dama na Najeriya, inda wasu shugabannin addinai ke yada labaran karya game da kwayar cutar da rigakafin ga miliyoyin mabiyansu.

Baya ga bayanan karya da ake yadawa a shafukan sada zumunta, wasu a arewacin Najeriya na tunawa da mutuwar yara da dama a shekarar 1996 sakamakon kamuwa da cutar sankarau a lokacin gwajin da Pfizer ke yi na maganin kwayoyin cutar ta baki, wanda ya yi sanadin tafka shari'a da katafaren kamfanin harhada magunguna da ya kai ga biyan diyya ga wasu iyalai.

“Amma ko shakka babu, akwai bukatar wasu jihohi su yi aiki tukuru wajen ganin cewa wadannan alluran rigakafin sun isa ga al’umma,” ya kara da cewa Najeriya na da alluran rigakafi miliyan 30 a hannu, inda da yawa za su isa nan da watanni masu zuwa.

XS
SM
MD
LG