Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Na Shirin Bada Rigakafin Covid-19 Mai Kara Kuzari Biyo Bayan Bullar Nau’in Omicron


Allurar rigakafin Covid 19

Najeriya za ta fara allurar rigakafin cutar COVID-19 mai kara kuzari na uku daga mako mai zuwa, in ji wani babban jami'i, bayan da kasar ta tabbatar da bullar nau’in Omicron ta farko a tsakanin matafiya biyu da suka zo daga Afurka ta Kudu a makon da ya gabata.

Babban daraktan hukumar kula da lafiya ta kasa Faisal Shuaib ya ce za a fara samun allurar rigakafin covid din mai kara kuzari na uku tun daga ranar 10 ga watan nan na Disamba ga wadanda aka yi wa cikakken rigakafin. Kashi 2.9 cikin 100 na ‘yan Najeriya wadanda suka riga suka yi allurar ne kadai suka cancanci yin allurar rigakafi kawo yanzu.

An fara ba da rahoto a kudancin Afirka mako guda da ya gabata, na nau’in Omicron – wani nau’in coronavirus wanda ke haifar da haɗarin kamuwa da cuta - ya kuma nuna rarrabuwar kawuna tsakanin manyan shirye-shiryen rigakafin a cikin ƙasashe masu arziki da ƙarancin rigakafin a cikin ƙasashe masu tasowa.

Gwamnati na shirin wata gagarumar fadakarwa ga al'ummarta da nufin su sami yin allurar.

Kasar ta sami kusan 5 miliyan na allurar AstraZeneca (AZN.L) a watan Oktoba daga COVAX daga wanda ta saya da kuma na gudummawa. Najeriya ta kuma yi alkawarin samar da allurai miliyan 11.99 da na miliyan 12.2 na Pfizer Inc/BioNTech da kuma Moderna Inc (MRNA.O).

Gwamnati ta sayi allurai kusan miliyan 40 na Johnson & Johnson (JNJ.N), in ji ta.

Shuaib ya ce za a samu allurar kara kuzari na uku ga wadanda suka "kammala allurai biyu na AstraZeneca, Moderna da Pfizer/BioNTech ko kashi daya na Johnson & Johnson."

Kasashe da dama sun sanya dokar hana zirga-zirga a kasashen kudancin Afirka, yayin da Hong Kong da Canada suka hana matafiya daga Najeriya. Koriya ta Kudu ta ce ta gano nau'in Omicron a cikin matafiya masu cikakken rigakafin da suka zo makon da ya gabata daga Najeriya.

XS
SM
MD
LG