Accessibility links

Akalla mutane 7 sun mutu a sakamakon wata fashewa a Kaduna

  • Jummai Ali

Masu aikin ceto dauke da wani wanda tashin bam ya rutsa dashi a birnin Kaduna, arewacin Nigeria. Laraban nan wani bam ya fashe a birnin Kaduna ya kashe akalla mutane 7.

Shedun gani da ido sunce wata fashewa a birnin Kaduna ta halaka akalla mutane bakwai ciki harda wani yaro dan shekara uku.

Saurari:
Hira da kwamishinan yan sandan jihar Kaduna, Bala Magaji Nasarawa akan tashin bam din.

Hirar da wani dan jarida Sama'ila Aruwa akan tashin bam din.

Shedun gani da ido sunce wata fashewa a birnin Kaduna, arewacin Nigeria ta kashe akalla mutane bakwai ciki harda wani yaro dan shekara uku.

'Yan sanda sunce nan da nan ba'a tantance abinda ya hadasa fashewar ba a yau Laraba, kodayake rahotanin farko da muka samu sun nuna cewa fashewar ta auku ne a kusa da gongonin gas.

Mutane da dama ne suka ji rauni kuma shaguna da dama sun lalace.

Ga hirar da muka yi da kwamishinan yan sanda jihar Kaduna da kuma wani dan jarida wanda yace shi yaje har wurin da wannan al'amari ya faru.

Ga gargadi nan, wadan nan hotuna suna da muni ainun har suna iya tayar da hankali sosai, sabo da haka a yi hattara.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG