Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akuffor-Ado Ya Tsame Hanunsa a Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa


Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

Shugaban Ghana Nana Dankwa Akuffo-Addo ya zabo wani babban lauya mai zaman kansa wanda ya shahara a sashen shari’ar kasar Ghana, mai suna Akoto Ampaw a matsayin mai shigar da kara na musamman ga gwamnati.

Idan wannan aiki ya tabbata, shi wannan lauya mai zaman kansa zai yi aiki ba tare da tsoma bakin wata hukuma ba, zai gudanar da bincike tare da shigar da kara a kan laifuffukan yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa karkashin wannan gwamnati ta NPP.

Ko shakka babu jama’a na ganin wannan mutumin da kima kuma ana kyautata masa zaton zai yi aiki da gaskiya da adalci kuma ba zai yi son zuciya ba a wannan aiki da aka bashi.

A lokacin yakin neman zaben shugaban kasa, Akofo-Addo ya yi alkawarin yaki da cin hanci da rashawa wanda ya zargi tsohuwar gwamnati da aikatawa kuma hakan na cikin manyan dalilai da ya sa al’umman kasar suka bashi ragama a zaben ranar 7 ga watan Disamban bara.

Sai dai gudun kada jama’a su zargeshi farautar jami’an tsohuwar gwamnati, Shugaba Akufo Addo ya yi alkawarin nada mai shigar da kara mai zaman kansa wanda ba ya cikin gwamnatinsa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00


Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG