Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Tsananin Talauci A Arewacin Najeriya-Masana


Almajirai
Almajirai

A Najeriya alamu na dada tabbatar da rahotannin da hukumar kididdiga ta kasar ke fitarwa a kan Jihohin da ke da matsanancin talauci musamman ma dai na yankin arewacin kasar.

Abin da ke nuna hakan shine yadda mabukata ke yin dafifi suna gogoriyo wajen karbar tallafi duk lokacin da aka samu wata kafa ta bayar da tallafi.

Mabukata suna fama wajen neman tallafi saboda su samu abin da zasu ci da iyalan su a wasu jihohin arewacin Najeriya duk da yake wasu gwamnoni na musanta cewa akwai matsanancin talauci a jihohin su.

Irin wannan yanayin bai rasa nasaba da yadda gwamnatoci da wasu daidaikun jama'a ke samar da tallafin abinci ga mabukata.

Gwamnatin Najeriya ma tana samar da abubuwan da zasu rage radadin fatara ga ‘yan kasar ta hanyar shirye-shirye daban daban a cewar ministan Abubakar Malami SAN.

To sai dai duba da yadda wasu ‘yan siyasa ke bayar da tallafi ga jama'a ya sa wasu na ganin suna yi ne domin manufar su ta siyasa, sai dai sakataren gwamnatin jihar Kebbi Babale Umar Yauri ya ce ba lallai ne hakan ya kasance ba.

Suma masu sharhi a kan lamurran yau da kullum na ganin akwai sahihiyar hanyar da tafi da cewa a taimaki jama'a ta yadda watakila za’a rage musu radadin talauci.

An jima ana ta fafatukar rage radadin fatara tsakanin ‘yan Najeriya sai dai har yanzu a iya cewa haka bata cimma ruwa musamman duba da yadda al’amurran talaka ke gudana a kasar.

Ga rahoton Muhammad Nasir daga Sokoto:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

XS
SM
MD
LG