Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mayakan al-Shabaab Zasu Yi Shigar Sojan Gona


Rundunar dakarun kiyaye zaman lafiya na kasashen Afirka a Somaliya, mai suna AMISOM, ta ce ta samu bayanan cewa mayakan al- Shabab za su sanya kayan soji irin na su domin kai hare-hare a wasu yankunan Somalia da ke hannun dakarun hadin gwiwar.

A cewar rundunar ta AMISOM, nufin mayakan na al-Shabab shi ne su gwara kan al’ummar Somalia da dakarunta, wadanda suka jima suna kare gwamnatin kasar na tsawon shekaru tara.

Rundunar sojin ta fitar da wannan sanarwar ce a shafinta na Twitter, inda ta kara da cewa mayakan na al-Shabab, sun samu kayan sojin ne a sansanin sojin Rundunar ta AMISON da su ka kaiwa hari a baya.

Akalla hare-hare uku mayakan na Al shabaab, suka kai a sansanonin dakarun hadin gwiwar na Afrika a kudancin Somalia cikin shekarar da ta gabata.

XS
SM
MD
LG