Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alherin Gaba Ya Fi Na Baya Yawa - Shugaba Buhari


Shugaba Buhari (Facebook/Bashir Ahmad)

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna nasarorin da kasar ta samu duk da kalubalen tsaro da koma bayan da annobar coronavirus ta haifar wa kasar.

Shugaba Buhari ya ce abin da ya faru a baya ya wuce, amma alherin da ke gaba yana da darajar gaske.

A wani rubutaccen sakon shugaban Najeriya na shiga sabuwar shekara ta 2022, ya bayyana damuwa ainun game da tabarbarewar tsaro inda ya mika ta'aziyarsa ga 'yan uwa da iyalan jami'an tsaro da fararen hular da suka rasa rayukansu sanadiyar rashin zaman lafiya.

Shugaba Buhari, wanda ya ce ya samar da kayan aiki da sake salon rundunonin tsaro don kare rayuka da dukiyar al’umma, ya nuna gwamnatinsa ba za ta yi kasa a guiwa ba, don tunkarar lamuran tsaro daje kan gaba a lamuran da ya fi maida hankali a kai.

Haka kuma shugaban ya jinjinawa Majalisar Dokoki don amincewa da dokar sashen Man Fetur PIB a takaice, da ta yi garambawul ga sashen, ya na mai cewa a bana gwamnatin sa za ta kara maida hankali kan kimiyyar yanar gizo wajen fadada hanyoyin tattalin arziki.

Ga shugaban matasa na tsohuwar jam’iyyar CPC da shugaba Buhari ya kafa Abubakar Maikudi, duk abun da shugaban ya aiwatar in dai ba ya bin sawu ba za a samu tasiri ba.

Shi kuma jigo a kamfen din shugaban Aminu Madaucin Bakori, ya aza alhakin wasu matakan da ke jawowa shugaban suka da rashin tasiri kan mukarrabai.

Shugaban dai zai share shekarar da bin kasafin kudi na Naira tiriliyan 17.1, ya yi korafi kan yanda ‘yan Majalisa su ka cusa aiyuka 6,576 a ciki,

Hakan na nuna kusan kowane dan Majalisa zai tashi da kimanin aiyuka 14 kasancewar yawan dukkan ‘yan Majalisar 469.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG