Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin 'Yan Majalisun Najeriya Zasu Iya Yin Watsi Da Karfin Ikon Shugaba Buhari Sakamakon Rashin Cewa Uffan A Game Da Kudirin Gyara Dokar Zabe


Nigeria Police Protest
Nigeria Police Protest

Shin 'Yan Majalisun Najeriya Zasu Iya Yin Watsi Da Karfin Ikon Shugaba Buhari Sakamakon Rashin Cewa Uffan A Game Da Kudirin Gyara Dokar Zabe?

‘Yan majalisar dokokin Najeriya sun bayyana cewa har yanzu shugaban kasa Muhammadu Buhari bai yi aiki kan kudirin gyaran dokar zabe da majalisar ta gabatar masa ba, domin amincewa da shi a kwanaki 30 da suka gabata.

A daren jiya lahadi ne aka cika wa’adin kwanaki 30 da 'yan majalisar suka ba shugaba Buhari domin ya duba tare da amincewa da kudirin don a zartar da shi zuwa doka.

To sai dai har zuwa lokacin rubuta wannan labari, babu wata sanarwa a hukumance zuwa ga majalisar dokokin kasar da kuma ‘yan Najeriya da ta fito daga fadar shugaban kasa kan makomar kudurin da ake sa ran zai taimakawa fannin gudanar da zabe idan gwamnati ta zartar da shi zuwa doka.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, sun gana a lokuta daban-daban da shugaba Buhari kan kudirin dokar tare da bayyana kwarin gwiwar cewa zai amince da shi.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar sun soki shugaba Buhari kan rashin cewa uffan ko amincewa da kudirin don zartar da shi zuwa doka kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A ranar 19 ga watan Nuwamba ne majalisar dokokin kasar ta mikawa shugaba Buhari kudirin domin ya amince da shi kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Sashe na 58 karamin sashe na 4 na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 wanda aka yiwa garambawul ya yi tandin cewa idan aka gabatar da kudirin doka ga shugaban kasa don amincewa, a cikin kwanaki 30 daga ciki zai nuna cewa ya amince ko kuma akasin haka.

A yayin da ‘yan siyasa da kungiyoyin fararen hula ke dakon matakin da shugaban Buhari zai dauka kan kudirin dokar, sai ga shi a makon da ya gabata ministan shari’a Abubakar Malami mai mukamin SAN, ya rubuta wasika zuwa ga shugaba Buhari, inda ya bayyana matsalolin da ke tattare da shigar da tsarin fidda-gwani kai tsaye a cikin kundin dokar zaben kasar.

Wata majiya da ta bukaci a sakaya suna, ta bayyana cewa a ranar Lahadi ne ya kamata shugaban ya tattauna da shugabannin majalisar, inda ake sa ran zai yi magana kan sashi na 87, wanda ya tanadi zaben fidda gwani kai tsaye.

Ana dai fuskantan rashin jituwa tsakanin ‘yan majalisar tarayya da gwamnonin jihohi kan batun shigar da zaben ‘yan takara kai tsaye a cikin kudirin zaben, inda ‘yan majalisar ke kara matsawa shugaban kasar lamba kan ya yi watsi da tanadin.

A ranar lahadi, kungiyoyin fararen hula daban-daban wato CSO’s, sun bukaci majalisar da ta yi watsi da karfin ikon shugaba Buhari, ta kuma zartar da kudurin zuwa doka ba tare da amincewar shugaban kasar ba.

Idan ana iya tunawa, a watan Yunin shekarar 2000 sai da majalisar dokoki ta Najeriya ta amince da kudirin dokar kafa hukumar raya yankin Neja-Delta wato NDDC da fiye da kashi biyu bisa uku na kuri’un da aka kada a majalisar, wanda hakan ya yi watsi da ikon shugaba Olusegun Obasanjo a lokacin.

Wasu 'yan majalisar dattawa sun shaida cewa kafin su fara hutun karshen shekara a wannan makon, majalisar dattawa za ta yanke shawara kan kudirin dokar zaben idan shugaban kasa ya ki amincewa da shi kamar yadda jaridar.

Auwal Musa Rafsanjani dake zama babban daraktan kungiyar CISLAC mai fafutukar kare hakkin fararen hula, kuma babban jami’in kungiyoyin kare hakkin bil adama na Transparency International da Amnesty International a Najeriya, ya ce duk da cewa Buhari bai ce uffan ba game da kudirin dokar zaben ba, a matsayinsu na wakilan jama'a, 'yan majalisar dokokin kasar sun yi abin da ya dace wajen zartar da mafi rinjayen fatan 'yan kasa zuwa ga shugaban Buhari.

Rafsanjani ya ce a halin yanzu matakin da ‘yan majalisar dokokin kasar za su dauka sakamakon shirun da shugaba Buhari ya yi kan kurdirin dokar zaben, zai tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa su ba yan amshin shata ba ne.

Wasu yan Najeriya a kafaffen sada zumunta ma sun yi ta tofa albarkacin bakinsu kan lamarin inda wasu ke ganin laifin shugaba Buhari saboda rashin cewa uffan kuma wasu ke ganin ya kamata a sake nazari kan kudurin don rashin kayan aiki na zamani da zai tabbatar da an gudanar da sahihin zabe.

XS
SM
MD
LG