Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Ina Isra'ilawa da Palastinawa Suka Kwana?


Mayakan sa kan Palestine.
Mayakan sa kan Palestine.

​Shugaban Amurka Barack Obama yace wata kila lokaci yayi na dakatarda tattaunawar zaman lafiya tsakanin Israila da Palastinawa a lokacin da bangarorin guda biyu suke nazarin inda aka kwana.

Mr. Obama ya gayawa manema labarai yau Juma’a a ziyarar wucin gadi da yake kaiwa Koriya ta Kudu cewa duka bangarorin zasu amfana idan suka nemi zaman lafiya, amma babu ko bangare daya da ya nuna zuciyar yanke shawarwari masu wahala a siyasance.

Yayi wannan kalami ne kwana daya bayan da kwamitin tsaron Isra’ila ya yanke shawarar dauke hannunsa daga teburin shawarwari da Palastine, domin mayarda ta martani akan matakin da kishiyoyin kungiyoyin Fatah da Hamas suka dauka na hade kawunansu domin samar da gwamnati daya.

Mr. Obama yace hada kai da kungiyoyin Palastine din su biyu suka yi bazai taimaka ba, amma shgaban yace gwamnatinsa baza ta mika wuya ba game da batun neman sasantawa da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yake jagoranta.

Bayan tattaunawa na tsawon sa’o’i shida Alhamis dinnan, gwamnatin Isra’ila ta fitar da sanarwar cewa “Isra’ila zata dauki mataki biyo bayan abunda Palestine tayi.”
Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG