Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi Bangarori A Hong Kong Su Kai Zuciya Nesa


Sakataren harkokin wajen Amurka, MikePompeo

Amurka ta bayyana matukar damuwarta na ci gaba da samun rashin zaman lafiya a siyasance da kuma rikici a yankin Hong Kong.

Amurka ta bayyana damuwarta ne bayan da aka samu arangama tsakanin ‘yan sanda da kuma masu zanga zanga da ta kara tsamari a ‘yan kwanakin nan da suka gabata.

“Muna sake kira ga dukkan bangarori a yankin Hong Kong da su kwantar da hankali. Tashin hankali daga dukkan bangarorin ba za mu yadda da shi ba. Gwamnatin yankin Hong Kong ita ce take da alhakin samar da zaman lafiya a Yankin Hong Kong,” Sakataran harkokin Wajan Amurka ya bayyana hakane a lokacin da yake ganawa da manema labarai a takaice a ma’aikatar harkokin waje ta Amurka.

Jawabin na Pompeo yana zuwa ne a daidai lokacin da ake kara samun tashin hankali, da ‘yan sandan Hong Kong suke barazanar yin harbi da harsashen gaske, idan masu zanga zangar basu daina amfani da makamai ba a sabuwar zanga zangar kin jinin gwamnati.

“Jami’an tsaro su kadai ba za su iya warware rashin zaman lafiya da tashin hankalin ba. Dole ne gwamnati ta dauki kwararan matakai don magance damuwar jama’a,” a cewar babban jami’in diflomasiyyar Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG