Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Shirya Zaman Tattaunawa Da Iran


Amurka ta shirya ba tare da wani sharadi ba ta tattaunawa da Iran domin kawo karshen tankiya tsakanin kasashen biyu, inji sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo a jiya Lahadi, amma kuma ya bayyana shakku ko Tehran zata amince da wata sabuwar tattaunawa.

Ya ce mun shirya mu shiga tattauna bada wasu sharuda kafin tattaunawar ba. Mun shirya mu zauna dasu. Pompeo yana fadawa manema labarai a Switzerland. Sai dai babban jami’in diplomasiyar Amurkan, ya kara da cewa yunkurin Amurka na kawo karshen miyagun ayyukan da wannan janhuriyar Islamiya hali ke yi zai ci gaba.

Ya ce lallai Amurka ta kimtsa tsaf tayi koma kan teburin tattaunawa idan Iraniyawan sun amince zasu sauya halayensu kamar kowace kasa.

Amma ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya fada a wata hira da labaran ABC a nan Amurka, cewa yin wata sabuwar tattaunawa da Washington abu ne da kamar wuya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG