Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Dora Haraji A Kayan Mexico A Matsayin Jan Kunne Ga Kwararan Bakin Haure


Trump
Trump

A kokarin daukar matakan hana kwararar bakin haure zuwa Amurka, Shugaba Donald Trump ya fada a shafinsa na twitter da yammacin jiya Alhamis cewa, Amurka zata kakabawa kayan kasar Mexico harajin kashi biyar cikin dari, wanda zai fara aiki a ranar goma ga watan Yuni.

A cewar Trump ranar goma ga watan Yuni ne, Amurka zata saka harajin kashi biyar cikin dari a kan dukkanin kayayyakin kasar Mexico da suke shigowa kasar mu, har sai lokacin da bakin haure suka daina shigowa kasar mu ta Mexico sannan mu cire harajin.

Trump ya fada a sakon twitter cewa harajin da zai karu a ranar daya ga watan Yuli zai ci gaba da karuwa har sai ya kai kashi 25 cikin dari kafin daya ga watan Oktoba, idan ba a magnace batun kwararan bakin hauren ba.

Ya kara da cewa zai cire harajin idan har aka shawo kan mataslar bakin hauren.

Da safiyar jiya Alhamis Tump, yace yana shirya yin wani babban jawabi a kan batun iyakar.

A baya Shugaban ya zargi kasar Mexico da rashin daukar kwararan matakan hanawa bakin haure dake fitowa daga kasashen tsakiyar nahiyar kudancin Amurka shiga Amurka ta kasar ta shiga Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG