Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Zargi Iran Da Kai Hari Akan Tankokin Hadaddiyar Daular Larabawa


John Bolton

A yau Laraba, mai ba da shawara kan harkokin tsaron Amurka, John Bolton, ya ce, yana da tabbacin Iran ce ta kai harin da aka yi a farkon wannan watan, a kan wasu tankokin man fetur da ke gabar tekun Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sai dai kuma da yake jawabi ga manema labarai yayin ziyarar da ya kai Abu Dhabi, saboda abin da ya kira tattaunawa a kan "muhimman batutuwa masu alaka da tsaro a yankin," Bolton bai bayar da wata hujjoji ba.

Amma ya kare zargin nasa akan Iran, inda ya ce, an harba nakiya mai fashewa akan tankokin man fetur.

Iran ta yi watsi da zargin da ake mata na cewa ita ta kai wannan harin, kuma a yau Laraba mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje Abbas Mousavi ya ce Iran ba za ta amince da zargin da Bolton ya yi akan kasar ta ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG