A ta bakin Amurka, "Mu na goyon bayan hukumomin Nijeriya a yayin da suka fara bincike game da wadannan hare-haren, kuma muna kira ga 'yan kasar su goyi bayan wannan kokari ta hukumomin kasar na ganin an gurfanar da wadanda su ka aikata wadannan laifuka a gaban shari'a."
Amurka dai na cigaba da goyon bayan mutanen arewacin Nijeriya a fafatukar da suke yi na dakile tsattsauran ra'ayi mai haddasa tashin hankali, da kuma taimaka wa gwamnatin Nijeriya a kokarinta na yin fito-na-fito da barazanar da kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnah Lid-Daawati wal Jihad da sauran kungiyoyi masu alaka da ita.