Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: 'Yan Majalisar Dattawa Za Su Kada Kuri'a Kan Alex Tillerson


Yau kwamitin majalisar dattawan Amurka mai kula da harkokin waje zai kada kuri’a kan Alex Tillerson, mutumin da shugaba Donald Trump ya zaba a matsayin Sakataren harkokin wajen kasar.

Sai dai har yanzu babu wata alama da ke nuna ko Sanata Marco Rubio na Jam’iyar Republican zai goyi bayan zabin na Tillerson.

A jiya Lahadi, wasu gaggan ‘yan jam’iyar ta Republican su biyu- wato Sanata John McCain da Lindsey Graham suka nuna goyon bayansu akan zabin na Tillerson, wanda a farko suka nuna shakkunsu saboda alakar da ya ke da ita da Rasha.

Sai duk da cewa goyon bayan McCain da Graham zai karawa Tillerson armashi, akwai damuwar cewa babu ko daya daga cikinsu dake cikin kwamitin mai kula da harkokin wajen Amurka.

Shi dai Sanata Rubio na Jihar Florida ya na cikin wannan kwamiti, amma har yanzu ya bai bayyana matsayarsa ba kan zabin na Tillerson.

XS
SM
MD
LG