Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Biya Ma’aikata Bashin Da Suke Bi A Bauchi


Babban Masallacin Jumma'a na Bauchi

Yanzu haka a wasu jihohi a Najeriya ma’aikata sai murna da godiya suke ga gwamnatoci wanda suka hada dana tarayya dana jihohi, adalilin biyansu kudaden albashinsu da suka makale.

A jihar Bauchi baya ga biyan kudaden albashi uku ta biya kudin albashin wannan watan da bai kare ba, inda shugaban ma’aikatan jihar Bauchi ya tabbatar wa da wakilin Muryar Amurka Haruna Abdulwahab Mohammad, cewa sun biya bashin da ake binsu harma sun biya ma’aikatan su albashin wannan watan kafin babbar sallah tazo.

Duk da yake dai gwamnatin tarayya ta taimakawa da wasu jihohin kasar ta haka ne suka sami damar biyan ma’aikatan kudaden su, amma dai har yanzu akwai bashin kudade kan gwamnatin.

Wasu ma’aikata dai da wakilin Muryar Amurka ya zanta da su alokacin da ya ziyarce su a ingin fitar da kudi, sun nuna godiyar su ga Allah saboda sun fara ganin abinda suke nema wato adalci.

Sai dai a yayin da ma’aikata ke murna, ‘yan fansho sun bukaci shugaban kasa da ya taimaka musu ganin an biya su kudaden su na giratute, inda suka nuna cewa anyi shekara da shekaru ba’a biyan su, hakane yasa suke kira ga shugaban ya taimakawa jihohi domin ko a samu a biya su.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG