Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Bayanan Sirrin 'Yan Takarar Shugabancin Amurka


Shugaban Amurka Barack Obama yace doka ta umarci gwamnatinsa da ta bayar da bayanan sirri, ciki har da wanda aka sakaya ga ‘yan takarar shugabancin kasar.

Wannan ya hada da ‘yar jam’iyyar Democrat Hillary Clinton da na jam’iyyar Rebuplican Donald Trump, wanda Obama yace bai cancanci ya zama shugaban Amurka ba.

A tsawon shekara ana yakin neman zabe, Trump ya yi suna wajen watsi da rubutun da akeyi masa don ya karanta bainar jama’a, maimakon haka sai kawai ya fadi abin da ke cikin zuciyarsa, wanda yawancin lokuta ake ganin bai dace ba. Wanda hakan ke sa alamar tambaya ga yadda Trump ‘din zai yi amfani da bayanan sirrin da shugaban kasa zai basu.

A jiha Alhamis Obama ya fadawa wani mai neman labarai cewa “idan suna son su zama shugaban kasa, dole su fara rike kansu kamar shugaban kasa, wannan na nufin idan aka basu bayanan sirri dole su bi a hankali kar su bayyana su ga jama’a.”

Obama yace, Babban dalilin da ya sa ake baiwa ‘yan takara bayanan shine, domin tabbatar da cewa sabon shugaban da za a zaba daga Democrat ko Republican, bai taka ‘kafa ya shiga ofis ba tare da ya shirya ba.

XS
SM
MD
LG