Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Binciken Take Hakkin Bil'adama Da Ake Zargin Sojojin Najeriya Da Yi


Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai, yana duba fareti a lokacin kaddamar da baburan da sojoji zasu rika shiga daji da su wajen yakar 'yan Boko Haram
Babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Janar Tukur Buratai, yana duba fareti a lokacin kaddamar da baburan da sojoji zasu rika shiga daji da su wajen yakar 'yan Boko Haram

Bayan daukan wani lokaci yana shiry-shirye, Kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa domin ya binciki zargin da ake wa sojojin kasar na take hakkin bil'adama ya fara aiki.

Kwamitin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa domin gudanar da bincike kan zargin cin zarafin bil adama da aka ce sojojin kasar na aikatawa ya fara aiki.

Ana sa ran kwamitin zai binciki zarge-zargen da ake yi wa sojojin wadanda kungiyoyi kare hakkin bil adama suka yi ta korafi akai.

“Aikin nan shi ne a saurari mutanen kasar nan, a ji abinda suka fada, a tabbatar gaskiya ne ko ba Gaskiya ba, sannan akan wannan tabbacin mu fadi abinda ya kamata gwamnati ta yi.” In ji Farfesa Jibo Ibrahim, daya daga cikin mambobin kwamitin.

A nata banagaren kungiyar Amnesty Internaional wacce ta sha zargin sojojin Najeriyar da take hakkin bil adama, ta yi fatan kwamitin kada ya zama na jeka-na-yi-ka.

“Har ta kai ga a Najeriya, mutane sun dauka kwamiti, wata hanya ce ta shashantar da al’mari, ba wai a duba a yi gaskiya ba. Amma dai muna masu kyakyawan fata.” In ji Isa Sanusi na kungiyar ta Amnesty.

Dubban sojoji na wurare daban-daban a birane da garuruwan Najeriya, inda aka jibge su ko dan samar da zaman lafiya ko kuma suna zaune a barikinsu.

Hakan ya sa, sukan yi hulda da sauran fararen hula a harkokinsu na yau da kullum.

Kungiyoyi kare hakkin bil adama irinsu Amnesty International sun sha sukar lamirin sojojin inda suke zarginsu da wuce makadi da rawa yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Saurari cikakken rahoton wakilinmu Sale Shehu Ashaka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG